Jumma’a, Nuwamba 27, 2015 Karfe 07:20

Labarai / Sauran Duniya

Za'a Tsaurara Wa Korea ta Arewa Takunkumai

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya kennan a lokacin da suke ganawa akan Korea ta Arewa. Junairu, 22 2013. (AP Photo/Mary Altaffer)Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya kennan a lokacin da suke ganawa akan Korea ta Arewa. Junairu, 22 2013. (AP Photo/Mary Altaffer)
x
Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya kennan a lokacin da suke ganawa akan Korea ta Arewa. Junairu, 22 2013. (AP Photo/Mary Altaffer)
Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya kennan a lokacin da suke ganawa akan Korea ta Arewa. Junairu, 22 2013. (AP Photo/Mary Altaffer)
Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya bada umarnin a tsaurara takunkumin karya tattalin arziki kan Korea ta Arewa saboda harba roka da ta yi cikin watan Disemba, mataki da ya sa Korea ta Arewa ta kangare har da nuna alamun cewa zata ma yi gwajin nukiliya.

Wakilan kwamitin su goma sha biyar baki dayansu jiya talata suka kada kuri’ar yin Allah wadai da harba kumbon, suna masu cewa ai gwajin makami mai linzami ne da aka haramta mata a karkashin kudurorin Majalisar Dinkin Duniya kan kasar da suke aiki yanzu.

Haka kuma kwamitin ya yi barazanar daukan karin “matakai masu tsanani”, idan Korea ta Arewa ta kaddamar da wani gwajin.

Nan da nan kuwa Korea ta Arewa ta maida martani, cewa ba zata sake shiga shawarwari da nufin kawarda dukkan harkokin nukiliya a zirin koriya ba. Daga nan ta yi alwashin zata habaka matakan soji da nukiliyarta a matsayin kariya, kalaman da wasu suka fassara a matsayin barzanar gwajin makamin nukiliya.

A lokutan baya, har sau biyu, Korea ta Arewan ta yi gwajin makaman nukiliya bayan da Majalisar Dinkin Duniya ta kakabata mata takunkumi bayan ta harba kumbo zuwa sararin subahana. Hotuna da taurarin dan adam suka dauka a baya-bayan nan sun nuna cewa kasar tana shirin yin gwaji na uku.

Sauti

 • Shirin Safe
  Minti 30

  Shirin Safe

  Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

 • Shirin Dare
  Minti 30

  Shirin Dare

  A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

 • Yau da Gobe
  Minti 30

  Yau da Gobe

  Yau da Gobe

 • Shirin Rana
  Minti 30

  Shirin Rana

  Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

 • Shirin Hantsi
  Minti 30

  Shirin Hantsi

  Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

Karin Bayani akan Shirya-shirye
Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
 
Karin Bayani akan Shirya-shirye