Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Majalisar Dokokin Amurka Sun Caccaki Hillary Clinton


Hoton Sakatariya Hillary Clinton kennan a lokacin da take gaban majalisar dokokin Amurka.
Hoton Sakatariya Hillary Clinton kennan a lokacin da take gaban majalisar dokokin Amurka.
Ahalinda ake ciki kuma ‘Yan majalisar dokokin Amurka sun caccaki babbar jami’ar difilomasiyyar Amurka saboda harin da aka kai kan karamin ofishin jakadancin Amurka dake Bengazi a Libya, daga nan suka yi gargadin cewa Amurka ba ta da manufa dangane al’amura da suke wakana a kasashe dake yammacin Afirka.

A karo na farko sakatariya Clinton ta bada shaida gaban kwamitin kula da harkokin kasashen waje dangane da harin da aka kai kan ofishin Amurkan dake Libya a ranar 11 ga watan satumban bara.

Cikin manyan masu sukar lamarin sakatariya Clinton, har da tsohon dan takarar shugabancin Amurka senata John McCain. Da yake magana shi ma senata Bob Corker, dan jam’iyyar Republican daga jihar Tennessee, yace gazawar da aka samu ta fuskar tsaro alama ce ta irin manyan matsaloli da ake fuskanta a ama’aikatar.
XS
SM
MD
LG