Jumma’a, Afrilu 29, 2016 Karfe 11:04

  Labarai / Afirka

  Wani Reshen Ansar Dine Zai Balle Kuma Ya Nemi Sulhu A Mali

  Hoton Alghabass Ag Intalla, shugaban wakilan Ansar Dine a lokacin da yake ganawa domin neman sulhu da shugaban Burkina Faso Blaise Compaore. Nowamba 16, 2012 a birnin Ouagadougou. Hoton Alghabass Ag Intalla, shugaban wakilan Ansar Dine a lokacin da yake ganawa domin neman sulhu da shugaban Burkina Faso Blaise Compaore. Nowamba 16, 2012 a birnin Ouagadougou.
  x
  Hoton Alghabass Ag Intalla, shugaban wakilan Ansar Dine a lokacin da yake ganawa domin neman sulhu da shugaban Burkina Faso Blaise Compaore. Nowamba 16, 2012 a birnin Ouagadougou.
  Hoton Alghabass Ag Intalla, shugaban wakilan Ansar Dine a lokacin da yake ganawa domin neman sulhu da shugaban Burkina Faso Blaise Compaore. Nowamba 16, 2012 a birnin Ouagadougou.
  Wani reshe na kungiyar ‘yan kishin Islama ta Ansar Dine ta kasar Mali yace shi kam zai balle, ya je ya kafa tasa kungiya mai zaman kanta wacce kuma zata nemi hanyar sulhunta rikicin da ake yi da su a kasar Mali.

  Haka kuma a cikin sanarwar da ta bada a yau, wannan sabuwar kungiyar dake kiran kanta Kungiyar Kishin Islama ta Azawad tace ita ma zata fito ta yaki duk wata akida ta masu tsatsauran ra’ayin addini.

  Ita dai kungiyar Ansar Dine ta hade ne da jinsunan Azbinawa da suka kwace yankin arewancin Mali bayan juyin mulkin da aka yi kasar a watan Maris na shekarar da ta gabata.

  Daga baya ne Ansar Dine din tareda kungiyoyin da take kawance da su suka kwace yankin baki daya, kuma suka daura damarar shimfida mishi tsarin shari’ar Islama mai gauni zallanta.

  Izuwa karshen watan Disamban da ya wuce ne Ansar Dine tace ta yarda ta yi sulhu da gwamnati amma kuma daga baya ta janye niyyar neman sulhun bayanda ta zargi gwanatin ta Mali da cewa bada gaske take neman zaman lafiya da su ba.

  Sauti

  • Shirin Hantsi
   Minti 30

   Shirin Hantsi

   Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

  • Shirin Safe
   Minti 30

   Shirin Safe

   Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

  • Shirin Dare
   Minti 30

   Shirin Dare

   A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

  • Yau da Gobe
   Minti 30

   Yau da Gobe

   Yau da Gobe

  • Shirin Rana
   Minti 30

   Shirin Rana

   Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

  Karin Bayani akan Shirya-shirye
  Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
  Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
   
  Karin Bayani akan Shirya-shirye