Jumma’a, Fabrairu 12, 2016 Karfe 06:36

  Labarai / Sauran Duniya

  Za'a Janye Dokar Hana Mata Sojoji A Amurka Shiga Fagen Fama

  Mata a fagen fama.Mata a fagen fama.
  x
  Mata a fagen fama.
  Mata a fagen fama.
  Wani babbar kusar ma’aikatar tsaro Amurka ta Pentagon yace Sakataren harakokin tsaron Amura din Leon Panetta na dab da janye dokar nan dake hana wa mata sojoji shiga fagagen fama, a buga da su.

  Jami’in yace yau da rana ne Mr. Panetta zai bada sanarwar janye wannan hanin, wanda aka ce abu ne da tun lokacinda ya zama sakataren tsaron Amurka a 2011 yake kwadayin yayi. A cikin shekaru biyu kadai da suka gabata, sakataren ya bude wa mata kamar dubu 50 kofar shiga aikin soja din.

  Jami’in yace Panetta na shirin yanka wa manyan kwamnadojin Amurka wa’adin tabattarda an aiwatarda wannan sabon umurnin nashi kafin nan da watan Mayu, wanda in anyi haka, dubban dubatan sojoji mata dake rundunonin sojan kasa, na kundumubala, na sama da na ruwa duk zasu sami damar daukar bindiga suje yake-yake kamar ‘yan’uwasu mazaje.

  A halin aikin sojan Amurka dai, zuwa fagen fama da shiga yaki itace babbar hanyar da aka fi saurin samun ci gaba da mukamai, kuma mata sun dade suna cewa hana su zuwa fagen fama kamar nuna musu banbanci ne da toshe musu hanyar samun ci gaba.

  Sauti

  • Shirin Safe
   Minti 30

   Shirin Safe

   Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

  • Shirin Dare
   Minti 30

   Shirin Dare

   A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

  • Yau da Gobe
   Minti 30

   Yau da Gobe

   Yau da Gobe

  • Shirin Rana
   Minti 30

   Shirin Rana

   Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

  • Shirin Hantsi
   Minti 30

   Shirin Hantsi

   Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

  Karin Bayani akan Shirya-shirye
  Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
  Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
   
  Karin Bayani akan Shirya-shirye