Talata, Disamba 01, 2015 Karfe 21:04

Labarai / Sauran Duniya

Koriya Ta Arewa Na Shirin Yin Gwajin Makamin Nukiliya

Shugaban Koriya ta Arewa kennan, Kim Jong Un a lokacin da yake jawabin sabuwar shekara. Junairu 1, 2013. Shugaban Koriya ta Arewa kennan, Kim Jong Un a lokacin da yake jawabin sabuwar shekara. Junairu 1, 2013.
x
Shugaban Koriya ta Arewa kennan, Kim Jong Un a lokacin da yake jawabin sabuwar shekara. Junairu 1, 2013.
Shugaban Koriya ta Arewa kennan, Kim Jong Un a lokacin da yake jawabin sabuwar shekara. Junairu 1, 2013.
Koriya ta Arewa tace tana shirin sake yin wani gwaji na ukku na makaman nukiliya, kuma zata dada cilla rokokinta zuwa cikin sararin samaniya, duk don nuna jin takaicin matakan kuntata mata da tace Majalisar Dinkin Duniya na dauka.

A cikin sanarwar da ta bada ta hannun kampaninta na dillacin labaru, Koriya ta Arewa tace zata yi wannan ne don kawai ta bata wa babbar abokiyar gabata, Amurka, rai.

Sai dai sanarwar da Hukumar tsaro ta kasar ta bada, ba tace ga lokacinda Koriya zata aiwatarda wadanan gwaje-gwajen ba.

Amma an san cewa duk wannan barazanar ta Korea ta Arewa tana zuwa ne bayan kuri’ar da dukkan kasashen dake cikin Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya suka jefa ne, inda suka zartad da kudurin la’antar Koriya din akan rokokin da ta harba a watan Disambar da ya gabata, wanda ya saba wa kudurorin da aka sha yankewa da suka haramta mata kera duk wasu makamai ko fasahu masu alaka da nukiliya.

Sauti

 • Yau da Gobe
  Minti 30

  Yau da Gobe

  Yau da Gobe

 • Shirin Rana
  Minti 30

  Shirin Rana

  Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

 • Shirin Hantsi
  Minti 30

  Shirin Hantsi

  Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

 • Shirin Safe
  Minti 30

  Shirin Safe

  Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

 • Shirin Dare
  Minti 30

  Shirin Dare

  A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

Karin Bayani akan Shirya-shirye
Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
 
Karin Bayani akan Shirya-shirye