Asabar, Nuwamba 28, 2015 Karfe 14:02

Labarai / Afirka

Sojojin Mali Sun Kwato Birnin Gao

Sojojin Najeriya da Chadi zasu shiga birnin na Gao domin tabbatar da kwanciyar hankali a cikinsa a bayan da akia fatattaki mayakan dake ci9kinsa

Sojojin gwamnatin Mali a yankin arewacin kasarSojojin gwamnatin Mali a yankin arewacin kasar
x
Sojojin gwamnatin Mali a yankin arewacin kasar
Sojojin gwamnatin Mali a yankin arewacin kasar
Jami’an gwamnatin Faransa sun ce sojojin gwamnatin Mali dake samun tallafin sojojin Faransa sun kwato birnin Gao, tungar ‘yan tawaye masu kishin Islama dake da matukar muhimmanci a yankin arewacin kasar.

Ma’aikatar tsaron Faransa ta fada jiya asabar cewa wata tawaga ta sojojin Najeriya da Chadi, zata shiga birnin domin tabbatar da kwanciyar hankali cikinsa. Har ila nyau, ma’aikatar ta ce magajin gari na birnin Gao, wanda ya nemi mafaka a Bamako, babban birnin kasar ta Mali, zai koma birninsa.

Wakilin Muryar Amurka Idrissa Fall, yace kama birnin na Gao yana da muhimmanci sosai a saboda ya zamo hedkwatar kungiyoyin ‘yan tawaye dabam-dabam.

Tun da fari a jiya asabar din, sojojin Faransa da na Mali, sun kwace filin jirgin saman Gao da wata gada dake kusa da nan. Ministan tsaron Faransa, Jean-Yves le Drian, yace dakarun sun yi amfani da hare-hare ta sama da kuma ta kasa domin ragargaza rumbunan kayan fada da kayan sufuri na ‘yan tawayen.

A yayin da ake ci gaba da daukar matakan sojan a cikin kasar Mali kuma, jami’an tsaro na kasashen Kungiyar Tarayyar Tattalin Arzikin Afirka ta Yamma, ECOWAs ko CDEAO, sun gana a Abidjan a kasar Cote D’Ivoire domin tattauna yadda za a gaggauta girka sojojin yanki a Mali. Ministan tsaron Cote D’Ivoire, Paul koffi Koffi, yace jami’an ECOWAS sun kuduri aniyar tabbatar da yiwuwar hakan ba tare da bata lokaci ba, yana mai cewa, "abinda ke gabanmu yana da matukar muhimmanci a saboda ya shafi tabbatar da girka sojojin da aka yi alkawari cikin gaggawa." Yace a bayan haka, zasu nazarci bukatu na kayan aiki da yadda za a gaggauta kai su can.

Shi ma kwamandan rundunar sojojin hadin guiwar ta kasashen Afirka ta Yamma, janar Shehu Usman Abdulkadir, na Najeriya, ya halarci wannan taron, inda ya fadawa ‘yan jarida cewa aikin girka sojojin na tafiya sosai, sai dai ba zai ce ga ranar da za a kammala ba.

Har ila yau, Janar Abdulkadir yace yayi imanin ba za a samu wata matsala ba wajen hada hancin gudanar da ayyukan sojojin kasashen na Afirka, wadanda zasu fito daga kasashe masu magana da harsunan Ingilishi da Faransanci.

Kungiyar ECOWAs dai tana shirin tura sojoji dubu 3 zuwa Mali.

Watakila Za A So…

Shirin Hantsi

Shirin Hantsi

Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku da labarai da hirarraki, da sharhin jaridu kama daga Najeriya zuwa Nijar har Ghana, da kuma ra’ayoyinku.
Shirin Safe

Shirin Safe

Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da rahotanni da dumi-duminsu, sannan mu na gabatar da wasu shirye-shirye kamar Noma da Lafiya Uwar Jiki.
Shirin Dare

Shirin Dare

A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na yadda duniyar ta yini da rahotanni da dumi-duminsu, sannan mu kan bude muku layuka domin ku bugo ku bayyana mana ra’ayoyinku kan batutuwan da suka fi muhimmanci a wannan rana, ko kuma wadanda ke ci muku tuwo a kwarya.
Shirin Rana

Shirin Rana

Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai da dumi-duminsu daga kowace kusurwa ta duniya, musamman ma dai muhimman abubuwan da suka faru, ko suke faruwa a kusa da ku a wannan rana.

An rufe wannan dandalin
Sharhi/Ra'ayi
     
Babu sharhi ko daya har yanzu a kan wannan dandalin, rubuta guda domin zamowa na farko

Sauti

 • Shirin Hantsi
  Minti 30

  Shirin Hantsi

  Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

 • Shirin Safe
  Minti 30

  Shirin Safe

  Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

 • Shirin Dare
  Minti 30

  Shirin Dare

  A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

 • Yau da Gobe
  Minti 30

  Yau da Gobe

  Yau da Gobe

 • Shirin Rana
  Minti 30

  Shirin Rana

  Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

Karin Bayani akan Shirya-shirye
Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
 
Karin Bayani akan Shirya-shirye