Litinin, Mayu 02, 2016 Karfe 00:09

  Labarai / Najeriya

  Gwamnatin Najeria Tayi Allah Wadai da Barazanar 'Yan Tsageran Niger Delta

  Hoton wasu daga cikin 'yan tsageran Movement for the Emancipation for the Niger Delta, (MEND) da aka dauka Febwairu. 24, 2006 file photo.Hoton wasu daga cikin 'yan tsageran Movement for the Emancipation for the Niger Delta, (MEND) da aka dauka Febwairu. 24, 2006 file photo.
  x
  Hoton wasu daga cikin 'yan tsageran Movement for the Emancipation for the Niger Delta, (MEND) da aka dauka Febwairu. 24, 2006 file photo.
  Hoton wasu daga cikin 'yan tsageran Movement for the Emancipation for the Niger Delta, (MEND) da aka dauka Febwairu. 24, 2006 file photo.
  WASHINGTON, D.C -- Gwamnatin Najeria tayi Allah wadai da wata sabuwar barazana da kungiyar ‘yan tsageran nan ta yankin Niger Delta ko Movement for the Emancipation of Niger Delta wato MEND a takaice, tayi mata a baya-bayannan.

  Wannan kungiya dai ta dauki alhakin kai hare-hare akan kamfanonin mai, fashe-fashen bom, da satar mutane domin garkuwa da su tun shekara ta 2006.
   
  Wakiliyar Muryar Amurka daga Abuja Heather Murdock tace a cikin barazanar da kungiyar tayi a karshen makon da ya wuce, MEND tace tana shirin kaiwa jami’an Najeria hari, da kamfanonin Afirka ta Kudu, da ma’ajiyar man fetur, da kamfanonin tatar mai a Najeria har ma da ketare domin nuna fushinsu dangane da samun shugabansu da aka yi da laifi, Henry Okah, a Afirka ta Kudu.
   
  A makon da ya wuce ne, aka samu Okah da lafuffuka guda 13 da suke alaqa da wani fashewar bom a cikin mota, ta shekara ta 2010, har mutane 12 suka mutu a babban birnin Najeria Abuja.
   
  Jiya lahadi, Ministan yada labaran Najeria, Labaran Maku yayi Allah wadai da barazanar wannan kungiya, kuma ya kira barazanar a matsayin kalaman marasa kishin kasa.
   
  Minista Mako yace abinda gwamnati take tsammani daga ‘yan Najeria shine nuna karin kishin kasa, da kuma sadaukarwa ga Najeria. Yace Najeria baza ta iya zama kasar da ba’a bin doka ba.
   
  Ana zargin Okah da shugabancin kungiyar MEND din, amma ya musanta hakan. A shekara ta 2010, ya kira kanshi a matsayin mai jimami a wata wayar tarho da yayi da kafar Al-Jazeera daga gidan yari a garin Johannesburg bayan da Najeria ta sa aka kama shi.

  Watakila Za A So…

  Tsaftar Ruwa Babbar Fa’ida Ce - Arc Abdullahi

  An lura cewa wata hanyar kare mutane daga cututtuka masu yawa ita ce tabbatar da tsafta, da lafiya da kuma ingancin ruwanda su ke sha. Karin Bayani

  Yau Ce Ranar Ma’aikata Ta Duniya

  Kamar kowace shekara, wannan shekarar ma ma'aikata a fadin duniya sun bayyana korafe-korafensu a wannan rana ta ma'aikata ta yau. Karin Bayani

  Obama Ya Halarci Taron Cin Abincin Dare Na Karshe Na KUngiyar 'Yan Jarida

  Wannan shine karo na takwas kuma na karshe da 'yan jarida masu aiki a fadar white suka a zamanin mulkin Obama Karin Bayani

  Za'a Iya Dasa Kan-Dan-Adam Kan Wata Gangar Jiki?

  Wasu likitoci suka ce wannan hauka ne kawai, kuma ba zai yi aiki ba. Karin Bayani

  Zika Ta Kashe Mutum Na Farko A Amurka.

  Mutumin dan shekaru 70 da haifuwa a watan febwairu ne ya kamu d a cutar da Zika. Karin Bayani

  Sauti

  • Shirin Rana
   Minti 30

   Shirin Rana

   Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

  • Shirin Hantsi
   Minti 30

   Shirin Hantsi

   Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

  • Shirin Safe
   Minti 30

   Shirin Safe

   Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

  • Shirin Dare
   Minti 30

   Shirin Dare

   A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

  • Shirin Rana
   Minti 30

   Shirin Rana

   Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

  Karin Bayani akan Shirya-shirye
  Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
  Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
   
  Karin Bayani akan Shirya-shirye