Talata, Fabrairu 09, 2016 Karfe 12:42

  Labarai / Sauran Duniya

  An Cigaba Da Shari'a Akan Harin Da Aka Kawo Wa Amurka

  Ana kara sauraron kararrakin harin da aka kawo wa a Amurka, ran 11 ga watan Satumbar shekarata 2001 a Guantanamo Bay. Ana kara sauraron kararrakin harin da aka kawo wa a Amurka, ran 11 ga watan Satumbar shekarata 2001 a Guantanamo Bay.
  x
  Ana kara sauraron kararrakin harin da aka kawo wa a Amurka, ran 11 ga watan Satumbar shekarata 2001 a Guantanamo Bay.
  Ana kara sauraron kararrakin harin da aka kawo wa a Amurka, ran 11 ga watan Satumbar shekarata 2001 a Guantanamo Bay.
  WASHINGTON, D.C. -- A yau ne ake sauraron karraraki a zagaye na biyu kennan akan mutane guda biyar da ake zargi da kitsa hare-haren ta’addanci na ran 11 ga watan Satumbar 2001 akan Amurka.
   
  A cikin masu kare kansu harda Khalid Sheikh Mohammed a zaman kotun da ake yi yau a sansanin sojin Amurka dake Guantanamo Bay, a kasar Cuba.
   
  Shari’o’in da za’a cigaba da yi masu tsayi, sune zasu tabbatar idan za’a yi wa wadanda ake zargi shari’a mai adalci.
   
  Lauyoyin wadanda ake zargi na so a yi watsi da kararrakin. Suna masu cewa jami’an gwamnatin Amurka sunyi amfani da hanyoyin da ba bisa ka’ida ba, domin uzzarawa wadanda ake zargi da amsa laifi wato, ta gana musu azaba kennan.
   
  Lauyoyin gwamnati zasu ce hanyoyin da aka yi amfani da su domin samun wadanda ake zargi da laifi daidai ne. Sannan zasu yi kokarin gani an cigaba da rufe asirin wuraren da wadanda ake zargi suka ce an gana musu azaba, kafin a tsare su kuma a kaisu Gwantanomo.
   
  Wasu shari’o’in da za’a gudanar a cikin wannan mako sun hada da ko za’a kira manya-manyan jami’an gwamnati su bada shaida? A ciki harda tsohon shugaban Amurka, George W. Bush.
   
  Wadanda ake zargi dai, na fuskantar laifuffuka sama da 3,000 na kisan kai.

  Sauti

  • Shirin Hantsi
   Minti 30

   Shirin Hantsi

   Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

  • Shirin Safe
   Minti 30

   Shirin Safe

   Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

  • Shirin Dare
   Minti 30

   Shirin Dare

   A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

  • Yau da Gobe
   Minti 30

   Yau da Gobe

   Yau da Gobe shiri ne mai inganta rayuwar matasa cikin fadakarwa da ilmantarwa da...

  • Shirin Rana
   Minti 30

   Shirin Rana

   Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

  Karin Bayani akan Shirya-shirye
  Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
  Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
   
  Karin Bayani akan Shirya-shirye