Talata, Satumba 16, 2014 Karfe 17:27

Afirka

Attajirin Afirka Ta Kudu Zai Taimaki Marasa Galihu

Gawurtaccen attajirin kasar Afirka Ta Kudu, Patrice Motsepe ya ce zai sadaukar da rabin dukiyar gidan su

Gawurtaccen attajirin kasar Afirka ta Kudu, Patrice Motsepe kenan a wani zaman tattaunawa a taron Davos
Gawurtaccen attajirin kasar Afirka ta Kudu, Patrice Motsepe kenan a wani zaman tattaunawa a taron Davos
Halima Djimrao-Kane
Gawurtaccen attajirin nan na kasar Afirka ta Kudu mai suna Patrice Motsepe ya ce zai bayar da rabin dukiyar gidan su ga gidauniyar tallafawa marasa galihu.

Motsepe, wanda ya mallaki kamfanin hakar ma’adanai na African Rainbow, ya bayar da sanarwar aniyar sa ta shiga sahun shirin masu alkawarin agazawa da ake kira “Giving Pledge” wanda Bill Gates mai kamfanin sadarwa na Microsoft da hamshakin dan kasuwannan Warren Buffett su ka kaddamar don karfafawa wadanda su ka fi arziki a duniya su yi kyauta da akalla rabin dukiyarsu.

Motsepe na daya daga cikin mutanen da su ka fi arziki a Africa. Mujallar Forbes da ke nan Amurka ta yi kiyasin cewa ya mallaki dukiyar da ta kai dala miliyan dubu biyu da digo sittin da biyar.

Mai kamfanin na hakar ma’adanai ya ce zai ba da rabin dukiyarsa ga Gidauniyar Motsepe, ta tallafawa marasa karfi wadda shi da matarsa su ka kafa a shekarar 1999 don agazawa ‘yan kasar Afirka ta Kudu marasa galihu.

A wata takardar yin bayani, Motsepe ya ce za a yi amfani da tallafinsa ne wajen inganta rayuwar mutane a ciki har da gajiyayyu da marasa ayyukan yi ko kuma wadanda ba a kula da su ba a cikin jama’a.
An rufe wannan dandalin
Sharhi/Ra'ayi
     
Babu sharhi ko daya har yanzu a kan wannan dandalin, rubuta guda domin zamowa na farko

Rediyo/Sauti

Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +1-202-619-0548 ko kuma +1-202-619-0551.
Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +1-202-205-9942.
 

        Shirin Safe                 0500 - 0530 UTC

Audio       Rumbun Shiri                       Live 

        Shirin Hantsi            0700 - 0730 UTC

Audio       Rumbun Shiri                       Live  

        Shirin Rana                1500 - 1530 UTC

Audio        Rumbun Shiri                      Live  

        Shirin Dare                2030 - 2100 UTC

Audio        Rumbun Shiri                      Live