Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Kiwon Lafiya Ta Duniya Ta Ja Kunne Game Da Illar Gishiri


Gishiri
Gishiri

Hukumar ta bukaci jama'a su rage cin gishiri saboda yana daga cikin manyan abubuwan dake haddasa hawan jini wanda ke janyo ciwon zuciya

Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya, WHO, ta fito da sabbin ka’idojin dake yin kira da babbar murya ga dukkan al’ummar duniya da su rage yawan gishirin da suke ci, su kuma rika yin amfani da sinadarin Potassium a cikin abincinsu, ko su riki cin kayan abincin da suke da sinadarin ciki.

A cikin sanarwar da ta bayar jiya alhamis, hukumar ta kiwon lafiya a duniya ta ce ya kamata kowane balagagge ya rage yawan gishirin da yake ci a kowace rana, ya komo kasa da gram 5, wato kasa da karamin cokali guda, a rana. Har ila yau, hukumar ta bayar da shawarar cewa abincin da balagagge zai rika ci a kullum ya kunshi gram uku da rabi na sinadarin Potassium.

Hukumar WHO ta ce ta bayar da wannan shawara ce a wani yunkurin hana mutane shiga cikin kasadar kamuwa da ciwon hawan jini, daya daga cikin manyan abubuwan dake haddasa ciwon zuciya da toshewar hanyoyin jini.

Shi dai gishiri, ba wai kawai yana nan tamkar garin gishiri da ak saba gani ba ne, akwai shi da yawa duk da cewa ba a jin dandanonsa a cikin madara, kwai, da kuma kayayyakin kwalama da ake sarrafawa.

Sinadarin Potassium, mai rage hawan jini, ana samunsa sosai cikin kayan abinci kamar wake, da ‘ya’yan abinci dangin gyada, gurjiya, kashu, da ganyayyaki da ‘ya’yan itace irinsu alayyaho da ayaba.
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG