Laraba, Nuwamba 25, 2015 Karfe 11:12

Labarai / Sauran Duniya

Dan Kunar Bakin Wake Ya Kaiwa Masallacin Shi'a Farmaki

Wani dan sanda yana kare wajen da akayi kunar bakin wake. Wani dan sanda yana kare wajen da akayi kunar bakin wake.
x
Wani dan sanda yana kare wajen da akayi kunar bakin wake.
Wani dan sanda yana kare wajen da akayi kunar bakin wake.
Jami’ai a arewa maso gabashin Pakistan  sun ce wani dan kunar bakin wake ya kai farmaki a masallacin yan shi’a, inda ya kashe akalla mutane 19, fiye da 30 kuma suka raunata.

Hukumomi sun ce fashewar bam din da ya faru a birnin Hangu ya faru ne yayinda yan shi’a suka gama sallar jumma’a suke barin masallacin, amma wadanda abin ya rutsa da su sun hada  yan sunni da ke a masallacin da ke kusa da na yan shi’ar.

Birnin Hangu dai dama wuri ne da aka fi yawan tashin hankali musamman fada da yan shi’ar da basu da rinjayi, wadanda sune kashi 20 bisa dari din yan Pakistan. Mayakan sa kan sunni sun dauki  yan shi’a a matsayin wadanda ba sa bin cikakken koyin addinin.

Har Yanzu dai ba a sami wanda ya dau alhakin kai harin ba.

A halin da ake ciki kuma kafar yada labaran turkiyya ta bada ruhoton fashewar bam a wajen ofishin jakadancin Amurka a Ankara ya kashe mutum daya.

Har Yanzu ba a iya sanin dalilin wannan fashewar bam din ba.

Motocin yan kwana-kwana da na asibiti sun je wurin don aikin agajin gaggawa.

Sauti

 • Shirin Hantsi
  Minti 30

  Shirin Hantsi

  Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

 • Shrin Safe
  Minti 30

  Shrin Safe

  Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

 • Shirin Dare
  Minti 30

  Shirin Dare

  A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

 • Yau da Gobe
  Minti 30

  Yau da Gobe

  Yau da Gobe

 • Shirin Rana
  Minti 30

  Shirin Rana

  Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

Karin Bayani akan Shirya-shirye
Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
 
Karin Bayani akan Shirya-shirye