Jumma’a, Mayu 06, 2016 Karfe 02:39

  Labarai / Sauran Duniya

  Dan Takarar Shugaban Kasar Paraguay Ya Mutu

  Lino Oviedo da ake cacar baki kan tsayawarsa takara ya mutu bayanda jirgin helkwafta da yake ciki ya fadi, amma magoya bayansa su na shakkar yadda abin ya faru.

  Magoya bayan dan takarar shugaban kasa Lino Cesar Oviedo su na kuka a kofar inda aka kai gawarsa, Lahadi 3 Fabrairu 2013.Magoya bayan dan takarar shugaban kasa Lino Cesar Oviedo su na kuka a kofar inda aka kai gawarsa, Lahadi 3 Fabrairu 2013.
  x
  Magoya bayan dan takarar shugaban kasa Lino Cesar Oviedo su na kuka a kofar inda aka kai gawarsa, Lahadi 3 Fabrairu 2013.
  Magoya bayan dan takarar shugaban kasa Lino Cesar Oviedo su na kuka a kofar inda aka kai gawarsa, Lahadi 3 Fabrairu 2013.
  Wani dan takarar kujerar shugaban kasa da ake cacar baki a kan tsayawarsa takara a kasar Paraguay, ya mutu a faduwar wani jirgin saman helkwafta.

  Hukumomi sun ce Lino Cesar Oviedo, da wasu mutane biyu sun mutu a lokacin da jirgin saman helkwafta da suke ciki ya fadi cikin hadarin ruwan sama a yankin arewacin Paraguay a ranar asabar. Amma duk da rahoton cewa akwai gagarumin hadarin ruwan sama a lokacin, wasu daga cikin magoya bayan Oviedo sun ce su na tababar yadda jirgin ya fadi.

  Oviedo tsohon kwamandan rundunar sojojin kasar Paraguay ne, kuma ya shiga cikin juyin mulkin shekarar 1989 a lokacin da aka hambarar da dadaddiyar gwamnatin kama karya ta shugaba Alfredo Stroessner.

  Ya gudu daga kasar Paraguay a shekarar 1996, a bayan da gwamnati ta zarge shi da kulla makarkashiyar yin wani juyin mulkin. A shekarar 1999, lokacin yana zaman gudun hijira a waje, an yi zargin cewa shi ne ya kulla kashe mataimakin shugaban kasar Paraguay na lokacin, Luis Maria Argana, da aka yi.

  Daga bisani, Oviedo ya koma kasar Paraguay, inda aka jefa shi a kurkuku a saboda makarkashiyar juyin mulkin 1996, amma kuma kotu ta wanke shi daga sauran laifuffukan da aka tuhume shi da aikatawa.

  Al'ummar kasar Paraguay zasu zabi sabon shugaban kasa a watan Yuni. A watan Yunin bara, majalisar dattijan kasar Paraguay ta tsige shugaba Fernando Lugo daga kan kujerar shugabancin kasar, a bayan da ya umurci 'yan sanda da su kori manoma talakawa da suka mamaye wasu manyan gonaki. An kashe manoma 11 da 'yan sanda 6 a wannan yamutsin. Manoman sun yi ikirarin cewa filayen da suka mamaye an yi musu kwacensu ne ta hanyoyin da suka saba ma doka.

  Watakila Za A So…

  Sauti Najeriya Da Kamaru Sun Kulla Wasu Yarjejeniya Tsakaninsu

  Bayan ziyarar da shugaba Poul Biya na kasar Kamaru ya kai Najeriya, inda suka gana tare da shugaba Buhari, kasashen biyu sun dauki matakan kara dankon zumunci ta fuskar tsaro da cinikayya da kuma zamantakewa tsakaninsu. Karin Bayani

  Yan Bindigar Somaliya Masu Alaka Da ISIS Sun Kara Yawa

  'Yan bindigar Somaliya dinnan masu alaka da ISIS sun dada yawa, kuma su na samun tallafin kudi da na soji daga kasar Yemen, a cewar wani babban jami'in leken asirin tsaro na soji, a hirarsa da sashin Somaliyanci na Muryar Amurka. Karin Bayani

  Sauti A Jamhuriyar Domokaradiyar Congo An Gano Moise Katumbi Laifin Amfani Sojojin Haya

  Janhuriyar Dimokaradiyyar Congo ta kaddamar da bincike game da zargin da ake ma fitaccen dan adawar siyasa Moise Katumbi, na amfani da sojojin haya na kasar waje, a cewar jami'an gwamnati jiya Laraba. Karin Bayani

  Sauti Kamfanin Peugeot Na Wani Shirin Samarwa Ma’aikata Sabbin Motoci A Najeriya

  Kamfanin hada motocin Peugeot dake zama kamfanin hada motoci na farko a Najeriya, yace yana wani shiri da gwamnatin Kasar na ganin yan Najeriya musanman ma'aikata sun mallaki sababbin motocin hawa da nufin rage hatsura da ake alakantawa da motocin Takunbo. Karin Bayani

  Sauti Wasu Yan Jihar Inugu Na Son Fulani Makiyaya Su Bar Musu Yanki

  Rikicin dake ci gaba da afkuwa tsakanin Fulani Makiyaya da Masu Gonaki musamman a Kudu maso Gabashin Najeriya, na ci gaba da daukar hankula sanadiyar samun salwantar rayuka da akeyi. Karin Bayani

  Gwamnan Ohio ya janye daga neman takarar shugabancin Amurka

  Gwamnan jihar Ohio John Kasich ya janye daga takarar neman Shugabancin Amurka jiya Laraba, ya bar abokin hamayyarsa Biloniyan nan mai harkar gidaje kuma tauraron Talbijin Donald Trump, wanda ake hasashen zai zama dan takarar Republican. Karin Bayani

  An rufe wannan dandalin
  Yadda Ake Son Gani
  Sharhi/Ra'ayi
       
  by: ahmad modibbo Daga: jalingo
  04.02.2013 06:20
  mutuwar irin wadan nan jarabawa ce ga jam iya. Allah ya kawo masu wani a madadin shi

  Sauti

  • Shirin Dare
   Minti 30

   Shirin Dare

   A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

  • Yau da Gobe
   Minti 30

   Yau da Gobe

   Yau da Gobe

  • Shirin Rana
   Minti 30

   Shirin Rana

   Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

  • Shirin Hantsi
   Minti 30

   Shirin Hantsi

   Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

  • Shirin Safe
   Minti 30

   Shirin Safe

   Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

  Karin Bayani akan Shirya-shirye
  Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
  Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
   
  Karin Bayani akan Shirya-shirye