Lahadi, Fabrairu 07, 2016 Karfe 09:24

  Labarai / Sauran Duniya

  An Yi Gagarumar Girgizar Kasa a Tekun Pacific

  Wata babbar girgizar kasa mai karfin awo 8 ta jijjiga tsibiran Solomons da talatainin dare a yankin tekun Pacific

  Wani masanin ilimin kimiyya na duba na'urar daukan girgizar kasa da auna karfin taWani masanin ilimin kimiyya na duba na'urar daukan girgizar kasa da auna karfin ta
  x
  Wani masanin ilimin kimiyya na duba na'urar daukan girgizar kasa da auna karfin ta
  Wani masanin ilimin kimiyya na duba na'urar daukan girgizar kasa da auna karfin ta
  Halima Djimrao-Kane
  Wata gagarumar girgizar kasa mai karfin awo 8 ta afkawa tsibiran Solomons a yau laraba, ta haddasa girgizar kasar karkashin teku wadda ka iya yin mummunar banna a yankunan gabar tekun kudancin Pacific.

  Cibiyar binciken fasali da yanayin  kasa ta Amurka ta ce da karfe daya da minti goma sha biyun dare girgizar kasar ta faru a kusa da tsibiran Santa Cruz a Solomons a karkashin kasa mai zurfin kimanin kilomita shida. Da ma tun a makon jiya yankin ya ke fama da motsin kasa.

  Haka nan kuma an kara yin wata kakkarfar girgizar kasa mai awo shida da digo hudu bayan ta farkon.

  A cikin rahotannin farko-farkon da suka fito daga Honiara, babban birnin tsibiran Solomons babu bayanin irin bannar da girgizar kasar ta yi.

  An yi kashedin afkuwar girgizar kasar karkashin teku a illahirin tsibiran Solomons, daga Vanuatu da Nauru da Papua New Guinea da Tuvalu da New Caledonia da Kosrae da Fiji da Kiribati da Wallis har zuwa Futuna.

  Cibiyar yin gargadin girgizar kasar karkashin teku ta Pacific ta ce gargadin ya hada har da wurare masu nisa kamar Hawaii, kuma New Zealand ta na cikin shirin ko ta kwana. Amma rahotannin farko sun ce ba a ga wata barazana ga Australia ba.

  Tsibiran Solomons na cikin yankin da aka yiwa lakabi da “Ring of Fire” wato “zoben wuta”, saboda fasalin karkashin kasar wurin mai yawan motsi da ke kewaye da tekun Pacific inda ke da yawan girgizar kasa da duwatsu masu aman wuta.
  An rufe wannan dandalin
  Sharhi/Ra'ayi
       
  Babu sharhi ko daya har yanzu a kan wannan dandalin, rubuta guda domin zamowa na farko

  Sauti

  • Shirin Hantsi
   Minti 30

   Shirin Hantsi

   Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

  • Shirin Safe
   Minti 30

   Shirin Safe

   Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

  • Shirin Dare
   Minti 30

   Shirin Dare

   A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

  • Shirin Rana
   Minti 30

   Shirin Rana

   Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

  • Shirin Hantsi
   Minti 30

   Shirin Hantsi

   Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

  Karin Bayani akan Shirya-shirye
  Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
  Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
   
  Karin Bayani akan Shirya-shirye