Jumma’a, Fabrairu 05, 2016 Karfe 23:05

  Labarai / Najeriya

  Najeria Ta Doke Mali 4-1

  Nigeria soccar players celebrate a goal against Mali. Wednesday, 6th Febuary 2013 (Reuters)Nigeria soccar players celebrate a goal against Mali. Wednesday, 6th Febuary 2013 (Reuters)
  x
  Nigeria soccar players celebrate a goal against Mali. Wednesday, 6th Febuary 2013 (Reuters)
  Nigeria soccar players celebrate a goal against Mali. Wednesday, 6th Febuary 2013 (Reuters)
  WASHINGTON, DC -- A karo na farko a shekaru 13, kungiyar kwallon kafan Najeria zata buga wasan karshe a gasar kofin nahiyar Afirka da akeyi a Afirka ta Kudu, bayan doke kungiyar kwallon kafar Mali a wasan kusa da karshe da ci 4 da 1.

  Dan baya Elderson Echiejile ne ya fara jefa kwallo a raga, minti 25 da sa wasa bayan wata kwana da Victor Moses ya aika. Bayan minti biyar kuma, Brown Ideye yayi arangama da mai kare ragar Mali, Mamadou Samassa a inda ya jefa kwallo na biyu a ragar Mali.

  Ci na uku kuwa, wani kwallon free kick da Emmanuel Emenike ya doka saura minti 3 a je hutun tsakar wasa ne ya daki kafar Momo Sissoko na Mali, ya canza hanya kana ya shiga raga. Ci na karshe ya zone daga Ahmed Musa bayan minti 60 da fara wasa, sannan Mali din ta ramo ci daya yayinda Cheick Diarra ya jefa kwallo a ragar Najeria minti 15 bayan cin da Musa yayi.

  Nasarar wannan wasa ya baiwa kungiyar Super Eagles din na Najeria damar karawa da duk wanda ya ci wasa tsakanin Ghana da Burkina Faso.

  Kwallon kafa a Najeria ya kasance tsin-tsiyar dake daure 'yan kasar baki daya. A duk lokacin da Najeria tayi nasara, mutane suna girke bam-bamce bam-bamcensu a gefe daya domin nuna farin cikinsu a matsayinsu na 'yan Najeria baki daya. Misalin wannan nasara itace ta gasar wasannin motsa jiki a turance Olympics, da akayi a shekara ta 1996, fagen da Najeria ta doke goggagun kasashe masu tarin fitattun 'yan kwallon kafa kamar Brazil da Argentina.

  Rabon Najeria da buga wasan karshe a wannan gasa tun shekara ta 2000 a inda kasar Cameroon tayi nasara a bugun fenariti da ci 4 da 3. Sau biyu Najeria tana cin kofin a wasan karshe, a shekara ta 1980 a gida Najeria, da kuma 1994  a Tunisia.

  Za'a doka wasan karshe ran 10 ga Fabrairu a filin wasa na FNB dake birnin Johannesburg.

  Watakila Za A So…

  Shirin Dare

  Shirin Dare

  A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na yadda duniyar ta yini da rahotanni da dumi-duminsu, sannan mu kan bude muku layuka domin ku bugo ku bayyana mana ra’ayoyinku kan batutuwan da suka fi muhimmanci a wannan rana, ko kuma wadanda ke ci muku tuwo a kwarya.
  Shirin Rana

  Shirin Rana

  Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai da dumi-duminsu daga kowace kusurwa ta duniya, musamman ma dai muhimman abubuwan da suka faru, ko suke faruwa a kusa da ku a wannan rana.
  Shirin Hantsi

  Shirin Hantsi

  Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku da labarai da hirarraki, da sharhin jaridu kama daga Najeriya zuwa Nijar har Ghana, da kuma ra’ayoyinku.
  Shirin Safe

  Shirin Safe

  Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da rahotanni da dumi-duminsu, sannan mu na gabatar da wasu shirye-shirye kamar Noma da Lafiya Uwar Jiki.

  Sauti

  • Shirin Dare
   Minti 30

   Shirin Dare

   A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

  • Yau da Gobe
   Minti 30

   Yau da Gobe

   Yau da Gobe

  • Shirin Rana
   Minti 30

   Shirin Rana

   Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

  • Shirin Hantsi
   Minti 30

   Shirin Hantsi

   Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

  • Shirin Safe
   Minti 30

   Shirin Safe

   Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

  Karin Bayani akan Shirya-shirye
  Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
  Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
   
  Karin Bayani akan Shirya-shirye