Laraba, Nuwamba 25, 2015 Karfe 05:11

Labarai / Sauran Duniya

Baza Muyi Sulhu Da Amurka Ba -Shugaban Addinin Iran

Shugaban addinin kasar Iran kennan, Ayatollah Ali Khamenei. (AP photo/Hasan Sarbakhshian/file)Shugaban addinin kasar Iran kennan, Ayatollah Ali Khamenei. (AP photo/Hasan Sarbakhshian/file)
x
Shugaban addinin kasar Iran kennan, Ayatollah Ali Khamenei. (AP photo/Hasan Sarbakhshian/file)
Shugaban addinin kasar Iran kennan, Ayatollah Ali Khamenei. (AP photo/Hasan Sarbakhshian/file)
Shugaban addinin kasar Iran yayi fatali da duk wata shawara ta a zo a zauna ayi wani taron sulhu tsakaninsu da Amurka akan maganar makamashin nukiliyar, yana mai cewa taron ba abinda zai tsinana.

A cikin shafinsa na duniyar gizo ta internet,  Ayatollah Ali Khamenei ya fada cewa Amurka na neman a zauna ayi magana amma kuma tana yiwa Iran barazanar kai mata hari, abinda yace ba zai taba razana Iran ba.

Mataimakin shugaban Amurka Joe Biden ne ya tado da maganar a jawabin da yayi wa wani taron harkokin tsaro a birnin Munich na Jamus, inda yake cewa a shirye Amurka take ta zauna tayi tattaunawar kai tsaye da Iran idan Iran din da gaske take son a warware wannan cece-kucce.

Kalaman Ayatollah Khamenei dai suna zuwa ne kwana daya bayanda aka fara aiwatarda wani sabon matakin da Amurka ta fito da shi na auna masana’antun man fetur na Iran da niyyar karya su.

Sauti

 • Shirin Dare
  Minti 30

  Shirin Dare

  A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

 • Yau da Gobe
  Minti 30

  Yau da Gobe

  Yau da Gobe

 • Shirin Rana
  Minti 30

  Shirin Rana

  Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

 • Shirin Hantsi
  Minti 30

  Shirin Hantsi

  Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

 • Shirin Safe
  Minti 30

  Shirin Safe

  Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

Karin Bayani akan Shirya-shirye
Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
 
Karin Bayani akan Shirya-shirye