Lahadi, Oktoba 04, 2015 Karfe 17:58

Labarai / Sauran Duniya

Shirgegen Dutse Daga Samaniya Zai Gitta Ta Kusa Da Duniya

Wannan dutse mai fadin mita 45 ko rabin filin kwallo, zai kusanci dunkiya fiye da wasu taurarin dan Adam na sadarwa a ran Jumma'a mai zuwa

Wanui curin Dutse mai suna Apophis dake yawo cikin sararin subhana. Irinsa zai kusanto duniya ranar Jumma'a 15 Fabrairu 2013Wanui curin Dutse mai suna Apophis dake yawo cikin sararin subhana. Irinsa zai kusanto duniya ranar Jumma'a 15 Fabrairu 2013
x
Wanui curin Dutse mai suna Apophis dake yawo cikin sararin subhana. Irinsa zai kusanto duniya ranar Jumma'a 15 Fabrairu 2013
Wanui curin Dutse mai suna Apophis dake yawo cikin sararin subhana. Irinsa zai kusanto duniya ranar Jumma'a 15 Fabrairu 2013
Hukumar Binciken sararin Samaniya ta Amurka, NASA, ta ce a mako mai zuwa, wani shirgegen dutse daga sararin subhana zai gitta ta kusa da kusa sosai da duniya, amma kuma babu wani abin tsoro, ba sai mutane sun sheka sun nemi mafaka cikin kogo ko ramukan karkashin kasa ba.

Wannan dutse zai wuce kimanin kilomita dubu 27 da 520 daga kan doron kasa ta bisan tekun Indiya da misalin karfe 7 da minti 24 na yamma agogon UTC, watau karfe 8:24pm agogon Najeriya, ranar jumma’a mai zuwa 15 ga watan Fabrairu. Masana kimiyyar samaniya na hukumar NASA wadanda suka auna falakin da wannan dutse mai fadin mita 45, ko rabin filin kwallon kafa ke bi, sun ce babu ta yadda zai ci karo da duniya.

Wannan dutse da zai gilma da sauri ba za a iya ganinsa da kwayar ido ba saboda ba ya da girma kuma yana da nisa daga doron kasa, amma masu tabaron hangen nesa zasu iya ganinsa kamar tauraro yana shigewa da sauri kusa da duniya fiye ma da wasu taurarin dan Adam na sadarwa.

Hukumar NASA ta ce wannan dutse na daya daga cikin mafiya girma da suka zo kusa sosai da duniyar bil Adama, amma shekaru aru aru da suka shige, wadanda suka fi shi girma ma sun sha fadowa kan duniya su na hallaka halitta da barna maras misaltuwa.

Irin wannan dutse na baya da yayi mummunar barna shi ne wanda ya fado kan dajin Tunguska a Siberia ta kasar Rasha a shekarar 1908, ya kwantar da bishiyoyi na tsawon daruruwan kilomitoci a kewayen inda ya abka.
An rufe wannan dandalin
Yadda Ake Son Gani
Sharhi/Ra'ayi
     
by: Bilya isah Daga: Kano nigeria
15.02.2013 15:48
Meye yai sana diyyar wucewar wannan dutse ta kusa da duniya


by: T. Salihi Daga: Kano
13.02.2013 19:37
wannan alama ce da ke kara nuna mana cewa karshen duniya yana kara kusantowa.Don haka wajibi ne 'yan uwa mu kara jin tsoron Allah da tuba bisa laifuffukan da muke aikatawa. Haka kuma mu gane cewa, addinin musuliunci shi ne addinin da yake addini a wajen Allah SWT. Don haka kada ka yarda ka mutu ba tare da ka zama musulmi ba.


by: Siraj Albani Jibia Daga: Jibia Nigeria
11.02.2013 20:18
Allah ya kare mu. Amin


by: Yaya Adamu Daga: Manila
11.02.2013 13:05
Allah mai kowa mai komai yana gunad da ababensa a boye da kuma bayyane, yana bada illimin a lokacin da yakeso, Allah karemu daga fitana da mummunar jarrabawa - Ameen

Sauti

 • Shirin Rana
  Minti 30

  Shirin Rana

  Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

 • Shirin Hantsi
  Minti 30

  Shirin Hantsi

  Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

 • Shirin Safe
  Minti 30

  Shirin Safe

  Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

 • Shirin Dare
  Minti 30

  Shirin Dare

  A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

 • Shirin Rana
  Minti 30

  Shirin Rana

  Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

Karin Bayani akan Shirya-shirye
Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
 
Karin Bayani akan Shirya-shirye