Asabar, Fabrairu 13, 2016 Karfe 07:45

  Labarai / Najeriya

  Gwamnatin Jihar Kano Ta Hana Bara Da Yawon Talla

  Mutane da babura a birnin Kano, dake arewacin Najeria. Mutane da babura a birnin Kano, dake arewacin Najeria.
  x
  Mutane da babura a birnin Kano, dake arewacin Najeria.
  Mutane da babura a birnin Kano, dake arewacin Najeria.
  WASHINGTON, D.C -- Gwamnatin jihar Kano ta hana yawon talla da bara a birnin Kano, daga ran Litinin 11 ga wannan wata.

  Wakilin Muryar Amurka daga jihar Kano, Muhammad Salisu Rabiu ya bayanna wannan sabuwar doka makonni biyu bayan hana daukar mutane akan babura da gwamnatin tayi.  

  Rahoton Muhammad Salisu yace gwamnatin tayi hakan ne da nufin tsaftace gari, hana 'yan mata yawon banza, da hana zubar da mutunci da bara ke janyowa.

  Ya kara da cewa wannan doka zai takali matsalar rashin zuwa makaranta da yara masu talla da bara ke fuskanta. Sannan duk wanda aka kama da karya wannan doka, zai biya tarar naira dubu biyar. 

  Birnin Kano dai na daya daga cikin birne a yammacin Afirka dake da tarin jama'a, kuma itace cibiyar hada-hadar kasuwanci a arewacin Najeria. Rashin kayan more rayuwa da ayyukanyi yasa mutane da yawa daga karkara suna kaura zuwa wannan birni domin neman na abinci. 

  Sufurin mutane akan babur da ake kira achaba, talla, da bara na daga hanyoyin da mutane masu dunbun yawa suke samun kudi, saboda rashin ilimi, ayyukanyi da nakasa. Dayawa daga cikin masu wadannan sana'o'i, ba'a san ransu sukeyi ba, sai don sun samu daman biyan bukatansu da tallafawa iyalansu.

  A lokacin da sama da kaso 50 cikin 100 na matasan Najeria ke fama da rashin ayyukanyi, manazarta na shakkar duk wani mataki da zai kara adadin marasa ayyukanyi saboda dalilan tsaro.

  Watakila Za A So…

  Shirin Safe

  Shirin Safe

  Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da rahotanni da dumi-duminsu, sannan mu na gabatar da wasu shirye-shirye kamar Noma da Lafiya Uwar Jiki.
  Shirin Dare

  Shirin Dare

  A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na yadda duniyar ta yini da rahotanni da dumi-duminsu, sannan mu kan bude muku layuka domin ku bugo ku bayyana mana ra’ayoyinku kan batutuwan da suka fi muhimmanci a wannan rana, ko kuma wadanda ke ci muku tuwo a kwarya.
  Shirin Rana

  Shirin Rana

  Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai da dumi-duminsu daga kowace kusurwa ta duniya, musamman ma dai muhimman abubuwan da suka faru, ko suke faruwa a kusa da ku a wannan rana.
  Shirin Hantsi

  Shirin Hantsi

  Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku da labarai da hirarraki, da sharhin jaridu kama daga Najeriya zuwa Nijar har Ghana, da kuma ra’ayoyinku.

  Sauti

  • Shirin Safe
   Minti 30

   Shirin Safe

   Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

  • Shirin Dare
   Minti 30

   Shirin Dare

   A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

  • Yau da Gobe
   Minti 30

   Yau da Gobe

   Yau da Gobe

  • Shirin Rana
   Minti 30

   Shirin Rana

   Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

  • Shirin Hantsi
   Minti 30

   Shirin Hantsi

   Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

  Karin Bayani akan Shirya-shirye
  Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
  Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
   
  Karin Bayani akan Shirya-shirye