Talata, Disamba 01, 2015 Karfe 17:26

Labarai / Najeriya

Wasu 'Yan Jarida Uku Sun Shiga Hannu A Kano

'Yan sanda sun kama 'yan jarida uku na gidan rediyon Wazobia dangane da kisan da aka yiwa masu aikin yin allurar rigakafin cutar shan inna a Kano

Hoton masu aikin yin allurar cutar shan inna su na shirin fara yiwa yara rigakafi a Kano, Najeriya Hoton masu aikin yin allurar cutar shan inna su na shirin fara yiwa yara rigakafi a Kano, Najeriya
x
Hoton masu aikin yin allurar cutar shan inna su na shirin fara yiwa yara rigakafi a Kano, Najeriya
Hoton masu aikin yin allurar cutar shan inna su na shirin fara yiwa yara rigakafi a Kano, Najeriya
Halima Djimrao-Kane
‘Yan sanda a arewacin Nageria sun kama ‘yan jarida uku da aka alakanta da kisan masu aikin yin allurar cutar shan inna tara a makon jiya a wani asibiti.

‘Yan jaridar wadanda ke aiki a gidan rediyon Wazobia FM ana zargin su ne da yin zugar da ta janyo kashe-kashen a cikin wata tattaunawar da su ka yi a rediyo kan shaci fadi da kuma jamhurun da ake yayatawa game da shirin rigakafin cutar shan inna.

Shugaban gidan rediyon, Sanusi Bello Kankarofi, ya ce da yammacin lahadi aka bukaci ‘yan jaridar uku su amsa kira a wani ofishin ‘yan sanda, kuma kwamishinan ‘yan sandan jahar Kano Ibrahim Idris ya tabbatar da kama su.

Ranar jumma’a wasu ‘yan bindiga a kan babura su ka kashe masu aikin yin allurar shan innar su tara, dukan su mata, sun rutsa su ne a lokacin da su ke kan aikin su na yin allurar cutar shan inna a wasu asibitoci biyu a cikin birnin Kano.

Babu tabbas game da wadanda su ka harbe ma’aikatan, amma an sha dora alhakin kai irin wadannan hare-hare kan kungiyar Boko Haram ta masu kishin Islama.

Wasu ‘yan arewacin Najeriya sun yi amanna cewa ana yin amfani da allurar polio ne don a hana mata haihuwa ko kuma ta na iya haddasa kamuwa da kwayar cutar kanjamau.

Najeriya na cikin kasashen duniya uku inda har yanzu ake samun cutar polio. A bara kasar ta bayar da rahoton samun yara dari da ishirin da daya da suka kamu da cutar, wanda shi ne adadin sabbin kamuwan da ya fi na ko'ina yawa a duniya.

wata yarinya mai suna Niima Ahmed wadda polio ta gurgunta a Kanowata yarinya mai suna Niima Ahmed wadda polio ta gurgunta a Kano
x
wata yarinya mai suna Niima Ahmed wadda polio ta gurgunta a Kano
wata yarinya mai suna Niima Ahmed wadda polio ta gurgunta a Kano

Watakila Za A So…

Shirin Rana

Shirin Rana

Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai da dumi-duminsu daga kowace kusurwa ta duniya, musamman ma dai muhimman abubuwan da suka faru, ko suke faruwa a kusa da ku a wannan rana.
Shirin Hantsi

Shirin Hantsi

Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku da labarai da hirarraki, da sharhin jaridu kama daga Najeriya zuwa Nijar har Ghana, da kuma ra’ayoyinku.
Shirin Safe

Shirin Safe

Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da rahotanni da dumi-duminsu, sannan mu na gabatar da wasu shirye-shirye kamar Noma da Lafiya Uwar Jiki.
Shirin Dare

Shirin Dare

A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na yadda duniyar ta yini da rahotanni da dumi-duminsu, sannan mu kan bude muku layuka domin ku bugo ku bayyana mana ra’ayoyinku kan batutuwan da suka fi muhimmanci a wannan rana, ko kuma wadanda ke ci muku tuwo a kwarya.

An rufe wannan dandalin
Yadda Ake Son Gani
Sharhi/Ra'ayi
     
by: Bilkisu
08.03.2013 14:30
Nifa gaskia na kasa gane gaskiyar lamaringa, ance taimakone ko? To ni Kuma nace banna so shin ina dalilin yi mun tilas?


by: muktar liman Daga: funtua
18.02.2013 21:22
wannan matsala ta najeriya. Babu abinda zamuce illa muyi kira ga dukkanin yan uwa musulmi. cewa mudage da addua. Mukoma zuwa ga Allah madaukakin sarki. Mutu ba ko ya tausaya mana amma ankai halin ha ulai.


by: muktar liman Daga: funtua
18.02.2013 21:22
wannan matsala ta najeriya. Babu abinda zamuce illa muyi kira ga dukkanin yan uwa musulmi. cewa mudage da addua. Mukoma zuwa ga Allah madaukakin sarki. Mutu ba ko ya tausaya mana amma ankai halin ha ulai.


by: Bello Usman Daga: Gombe
17.02.2013 11:12
Allah ya kawo Sawki Amen

Sauti

 • Yau da Gobe
  Minti 30

  Yau da Gobe

  Yau da Gobe

 • Shirin Rana
  Minti 30

  Shirin Rana

  Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

 • Shirin Hantsi
  Minti 30

  Shirin Hantsi

  Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

 • Shirin Safe
  Minti 30

  Shirin Safe

  Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

 • Shirin Dare
  Minti 30

  Shirin Dare

  A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

Karin Bayani akan Shirya-shirye
Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
 
Karin Bayani akan Shirya-shirye