Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Hana Makaman Kare Dangi Bata Cimma Yarjejeniya Ba Da Iran


Herman Nackaerts kennan na hukumar hana makaman kare dangi a lokacin da yake ganawa da 'yan jarida bayan dawowa daga Iran.Fabrairu 14, 2013.
Herman Nackaerts kennan na hukumar hana makaman kare dangi a lokacin da yake ganawa da 'yan jarida bayan dawowa daga Iran.Fabrairu 14, 2013.

Wani babbar kusa na Hukumar hana wanzuwar makaman kare dangi na nukiliya a duniya ya dawo hannu fayau daga Iran, ba tare da yarjejeniya ko daya ba akan yadda za’a gudanar da binciken gano ko Iran na kokarin kera wa kanta makaman nukiliya ko akasin haka.

Herman Nackaerts, wanda ya jagoranci tawagar wakilan hukumar ta IAEA a tattaunawar da suka yi da kusoshin gwamnatin Iran yace sassan biyu sun kasa cimma daidaituwar baki akan kulla duk wata yarjejeniya.

Sai dai kuma a yau Alhamis ma ance an ga karin alamomin dake nuna cewa lalle Iran tana kara bada kuzari wajen inganta ma’aikatu da fasahunta na nukiliya din.

Jaridar Washington Post ce ta ruwaito cewa a kwanakin da suka gabata Iran tayi kokarin sayo wasu dubban na’urorin masu kama da zobe daga China, wadanda za’a iya makallawa ga bututun makamai masu linzame.

An hana saida wa Iran irin wadannan zobbai a karkashin kudurorin Majalisar Dinkin Duniya. Ba dai tabbas na ko idan wannan yunkurin sayo zobban da Iran atyi, yaci nasara.
XS
SM
MD
LG