Jumma’a, Fabrairu 12, 2016 Karfe 21:19

  Labarai / Najeriya

  Wata Kungiya Ta Dauki Alhakin Sace 'Yan Kasashen Waje A Jihar Bauci

  Wata kungiya mai suna Jama'atul Ansarul Muslimina Fi Biladil Sudan ta bada sanarwar cewa ita tayi awon gaba da 'yan kasashen waje guda bakwai dake aiki a kamfanin gina titi a Najeria.

  Kwamishinan 'Yan Sanda na Jihar Bauchi, Mohammed Ladan, yana bayani ga 'yan jarida game da tashin bam a harabar majami'ar Harvest Field Church dake Unguwar Yelwa a Bauchi, lahadi 3 Yuni 2012Kwamishinan 'Yan Sanda na Jihar Bauchi, Mohammed Ladan, yana bayani ga 'yan jarida game da tashin bam a harabar majami'ar Harvest Field Church dake Unguwar Yelwa a Bauchi, lahadi 3 Yuni 2012
  x
  Kwamishinan 'Yan Sanda na Jihar Bauchi, Mohammed Ladan, yana bayani ga 'yan jarida game da tashin bam a harabar majami'ar Harvest Field Church dake Unguwar Yelwa a Bauchi, lahadi 3 Yuni 2012
  Kwamishinan 'Yan Sanda na Jihar Bauchi, Mohammed Ladan, yana bayani ga 'yan jarida game da tashin bam a harabar majami'ar Harvest Field Church dake Unguwar Yelwa a Bauchi, lahadi 3 Yuni 2012
  WASHINGTON, D.C --  Wata sanarwa dake dauke da sharuda guda biyu da kuma sunan Abu Usamatul Ansari, tayi bayanin cewa bisa irin cin mutunci da kasashen turawa suke aikatawa addinin Musulunci a Afghanistan da Mali, kunigyar tana rike da mutane guda bakwai da suka hada da  ma'aikata daga kasashen turawa da Lebanon masu aiki da kamfanin Setraco a Najeria.

  Wakilin Muryar Amurka, Abdulwahab Muhammad ya bada bayanin cewa kungiyar ta yi gargadin cewa duk wani yunkuri ko kuma wani shiri daga kasashen turawa ko gwamnatin Najeria da ya sabawa ka'idojinsu zai haifar da abubuwan da suka faru a baya.

  Kungiyar bata bayanna ko wadanne abubuwa ne suka faru a baya ba.

  A halin da ake ciki, manyan ma'aikatan kamfanin Setraco sun bar garin Jama'are kamar yadda shugaban karamar hukumar, Adamu Aliyu ya shaida wa Muryar Amurka. 

  "Su turawan da suke rage, wadanda basu fi su uku ba, sune suka tafi Abuja. Amma sauran kananan ma'aikata suna nan." A cewar shugaban karamar hukumar.   

  Kamfanin Setraco dai na aikin titin Kano zuwa Maiduguri ne a jihar bauci, kuma yana da sansani a garin Jama'are inda ma'aikatan ke kwana.

  Jiya Lahadi mun baku rahoton da yace, wasu 'yan bindiga sun kashe maigadin sansanin kamfanin, kuma sun yi awon gaba da mutane guda bakwai. 

  Satar mutane domin yin garkuwa da su ya zama ruwan dare a Najeria, al-amari wanda aka fi sani da faruwa a kudancin kasar, yanzu ya yadu zuwa kusan ko ina a Najeria.

  Najeria kasa mai fama da rashin ayyukanyi, rashin kayan more rayuwa, da lalacewar tsarin tsaro na fuskantar kalubalen tattalin arziki saboda karancin tituna masu kyau, karuwar adadin mutane, rashin kwararru masu horas da ma'akaita wadanda yawacinsu daga kasashen waje suke zuwa, da kuma tasowar kungiyoyi masu tsatsaurrar ra'ayi dake amfani da addini da makamai domin yada manufofinsu.

  A watan da wuce ne, wasu 'yan bindiga a Aljeriya su 30 suka yi garkuwa da ma'aikatan kasashen waje masu yawa a wani kamfanin sarrafa iskar gas, kuma hakan ya jawo hankalin duniya baki daya game da haduran da ma'aikatan kasashen waje ke fuskanta. Wannan arangama dai ta kare ne da mutuwar ma'aikatan kasashen waje guda 37, da duka 'yan bindigan su 30 bayan luguden wuta da sojojin kasar Aljerian suka yi musu.  

  Kwararru sun bayyana cewa rashin kayan more rayuwa kamar tituna na durkusar da tattalin arziki, saboda wahala, da lokacin da ake sharewa wajen sufurin mutane da kaya.

  Watakila Za A So…

  Shirin Rana

  Shirin Rana

  Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai da dumi-duminsu daga kowace kusurwa ta duniya, musamman ma dai muhimman abubuwan da suka faru, ko suke faruwa a kusa da ku a wannan rana.
  Shirin Hantsi

  Shirin Hantsi

  Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku da labarai da hirarraki, da sharhin jaridu kama daga Najeriya zuwa Nijar har Ghana, da kuma ra’ayoyinku.
  Shirin Safe

  Shirin Safe

  Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da rahotanni da dumi-duminsu, sannan mu na gabatar da wasu shirye-shirye kamar Noma da Lafiya Uwar Jiki.
  Shirin Dare

  Shirin Dare

  A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na yadda duniyar ta yini da rahotanni da dumi-duminsu, sannan mu kan bude muku layuka domin ku bugo ku bayyana mana ra’ayoyinku kan batutuwan da suka fi muhimmanci a wannan rana, ko kuma wadanda ke ci muku tuwo a kwarya.

  An rufe wannan dandalin
  Yadda Ake Son Gani
  Sharhi/Ra'ayi
       
  by: Abdullahi kafinta bulangu Daga: Bulangu K.H.S. JAHAR JIGAWA
  19.02.2013 00:30
  Allah yabamu zaman lafiya akasar mu najeriya da chigaba mai amfani

  Sauti

  • Yau da Gobe
   Minti 30

   Yau da Gobe

   Yau da Gobe

  • Shirin Rana
   Minti 30

   Shirin Rana

   Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

  • Shirin Hantsi
   Minti 30

   Shirin Hantsi

   Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

  • Shirin Safe
   Minti 30

   Shirin Safe

   Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

  • Shirin Dare
   Minti 30

   Shirin Dare

   A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

  Karin Bayani akan Shirya-shirye
  Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
  Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
   
  Karin Bayani akan Shirya-shirye