Laraba, Nuwamba 25, 2015 Karfe 21:17

Labarai / Sauran Duniya

Gwamna Ya Nemi Ayi Taron Duniya Kan Barazanar Duwatsu Daga Samaniya

Gwamnan Chelyabinsk inda wani dutse ya fado ranar Jumma'a yace kasa daya ba zata iya tunkarar irin wannan dutse kio wanda ya fi shi girma ba

Hoton wannan dutse lokacin da yayi bindiga wanda wani mutumi ya dauka daga cikin motarsa a kan hanyar zuwa Chelyabinsk, Jumma'a 15 Fabrairu 2013Hoton wannan dutse lokacin da yayi bindiga wanda wani mutumi ya dauka daga cikin motarsa a kan hanyar zuwa Chelyabinsk, Jumma'a 15 Fabrairu 2013
x
Hoton wannan dutse lokacin da yayi bindiga wanda wani mutumi ya dauka daga cikin motarsa a kan hanyar zuwa Chelyabinsk, Jumma'a 15 Fabrairu 2013
Hoton wannan dutse lokacin da yayi bindiga wanda wani mutumi ya dauka daga cikin motarsa a kan hanyar zuwa Chelyabinsk, Jumma'a 15 Fabrairu 2013
Gwamnan yankin Chelyabinsk na kasar Rasha, inda wani dutse daga samaniya ya fado yayi barna mai yawa, ya nemi shugabannin kasashen duniya da su je su yankin nasa domin tattauna yadda duniya zata hada hannu wajen daukar matakan kare irin wannan barazana a nan gaba.

Gwamnan yankin na Chelyabinsk, Mikhail Yurevich, yayi magana ta wayar tarho da ‘yan jarida dake birnin Moscow jiya litinin. Yace babu wata kasar da zata iya kaddamar da tsaro ta sama da ake bukata domin tare irin dutsen da yayi bindiga a daidai kan yankinsa a ranar jumma’a da ta shige, ko kuma wanda ma ya fi shi girma.

Bindigar da wannan dutse yayi a lokacin da ya shigo cikin iskar da ta kewaye duniya a daidai yankin, ta farfasa gilashin tagogin gidaje kusan dubu 5 a garin Chelyabinsk. Mutane fiye da dubu daya sun ji rauni a garin.

Wakilin yankin Chelyabinsk a babbar majalisar dokokin tarayya ta Rasha, Konstantin Tsybko, yace garin Chelyabinsk shi ne na farko a tarihi da ya tsira daga abinda ya kira “farmaki daga sararin samaniya.”

Har yanzu akwai mutanen garin da dama dake asibiti su na jinyar raunukan da suka samu lokacin da wannan dutse ya fado daga samaniya.
An rufe wannan dandalin
Sharhi/Ra'ayi
     
Babu sharhi ko daya har yanzu a kan wannan dandalin, rubuta guda domin zamowa na farko

Sauti

 • Yau da Gobe
  Minti 30

  Yau da Gobe

  Yau da Gobe

 • Shirin Rana
  Minti 30

  Shirin Rana

  Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

 • Shirin Hantsi
  Minti 30

  Shirin Hantsi

  Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

 • Shrin Safe
  Minti 30

  Shrin Safe

  Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

 • Shirin Dare
  Minti 30

  Shirin Dare

  A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

Karin Bayani akan Shirya-shirye
Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
 
Karin Bayani akan Shirya-shirye