Alhamis, Fabrairu 11, 2016 Karfe 15:59

  Labarai / Sauran Duniya

  Wani Makamin Yaki Da Sauro Yana Da Matsala Babba

  Masana sun gano cewa sauron su na iya sabawa da wani maganin da mutane ke shafawa a jikinsu na korar sauro bayan 'yan sa'o'i kadan kawai

  Sauro Yana Cizon Yatsar MutumSauro Yana Cizon Yatsar Mutum
  x
  Sauro Yana Cizon Yatsar Mutum
  Sauro Yana Cizon Yatsar Mutum
  Wani babban makamin da ake amfani da shi wajen yaki da sauro yana da wata babbar matsala. Masana sun gano cewa a cikin 'yan sa'o'i kadan kawai da fara shakar warin wani maganin da ake shafawa a jiki domin korarsu, sauron su na iya sabawa da shi har su jure masa.

  Masu bincike a Makarantar Nazarin Tsabta da Cututtukan Yankuna Masu Zafi ta London, sun fada cikin mujallar "Plos One" cewa wannan magani mai suna DEET da ake shafawa ko fesawa a jikin dan Adam domin korar sauro, yana aiki ne na tsawon sa'o'i uku kawai. Masanan sun yi amfani da wani sauro jinsin "Aedes aegypti" mai yada cutar zazzabin Dengue.

  Masanan sun gano cewa shakar wannan magani ta dan karamin lokaci, tana sa wasu daga cikin saurpon su fara jure masa, ta yadda a karo na biyu idan suka sake jin warin maganin na DEET, ba zasu kauce ba, kuma ba zai dame su ba.

  Jagoran masanan da suka rubuta wannan bayanin, James Logan, ya kwatanta wannan lamari da yadda dan Adam yake iya jure ma warin wani abu, kamar daddawa, ta yadda idan har ya jima yana ji, sai ya zo har kuma ba zai ji warin ba daga baya saboda sabo.

  ya jaddada cewa ba wai wannan sakamakon yana nufin cewa ya kamata mutane su daina yin amfani da DEET ko sauran magungunan korar sauro da kwari ba ne, musamman ma a yankunan da suka fi kasadar kamuwa da cuce-cucen da sauro ko kwari ke yadawa.

  A maimakon haka, ya bayar da shawarar da a bullo da sabbin dabarun yin amfani da wadannan magungunan wajen yakar sauro da sauran kwari.
  An rufe wannan dandalin
  Sharhi/Ra'ayi
       
  Babu sharhi ko daya har yanzu a kan wannan dandalin, rubuta guda domin zamowa na farko

  Sauti

  • Shirin Hantsi
   Minti 30

   Shirin Hantsi

   Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

  • Shirin Safe
   Minti 30

   Shirin Safe

   Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

  • Shirin Dare
   Minti 30

   Shirin Dare

   A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

  • Yau da Gobe
   Minti 30

   Yau da Gobe

   Yau da Gobe

  • Shirin Rana
   Minti 30

   Shirin Rana

   Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

  Karin Bayani akan Shirya-shirye
  Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
  Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
   
  Karin Bayani akan Shirya-shirye