Lahadi, Maris 29, 2015 Karfe 02:05

Afirka

Ana Tafka Fada A Birnin Gao

An yi musayar wuta tare da tada nakiyoyi a birnin Gao dake arewacin kasar Mali, inda dakarun kasar da na Faransa da kuma dakarun yammacin Afrika suke yakar mayakan kishin Islama.

Dakarun Mali a lokacin da suke zagaye a garin Gao. Fabrairu 20, 2013.Dakarun Mali a lokacin da suke zagaye a garin Gao. Fabrairu 20, 2013.
x
Dakarun Mali a lokacin da suke zagaye a garin Gao. Fabrairu 20, 2013.
Dakarun Mali a lokacin da suke zagaye a garin Gao. Fabrairu 20, 2013.
Jami’an ma’aikatar tsaron kasar Mali sun bayyana yau alhamis cewa, an fara musayar wuta ne bayan harin da mayaka suka kai a Gao da tsakar dare, dakaru kuma suka shiga birnin domin kakkabe su. Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya laburta cewa, an cinnawa babbar kotun dake birnin Gao wuta.
 
Wani kakakin ministan tsaro ya shaidawa muryar Amurka cewa, an kwato birnin sai dai har yanzu ana fuskantar matsalar tsaro a wurin.
 
A halin da ake ciki kuma, shaidu da dakarun  tsaro sun ce wani harin bom da aka kai kan wata mota a garin Kidal dake arewacin kasar ya jiwa a kalla mutane biyu rauni.
 
A wata sabuwa kuma, kamfanin dillancin labarai na Associated Press ya buga rahoto cewa, an kashe a  kalla mayaka 10 bayanda dakarun kasar Faransa suka bude wuta kan wata motar akori kura dake tafiya a arewacin Mali. Kamfanin dillancin labaran yace lamarin ya auku ne jiya Laraba yayinda rundunar ‘yan sanda ke farautar mayaka.

Audio Shirin Safe :         0500 - 0530 UTC

Audio Shirin Hantsi :      0700 - 0730 UTC

Audio Shirin Rana :        1500 - 1530 UTC

Audio Shirin Dare :         2030 - 2100 UTC

Audio Yau da Gobe:       1530 - 1600 UTC

Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12026190548 ko kuma +12026190551.
Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
 
Karin Bayani akan Sauti