Lahadi, Mayu 01, 2016 Karfe 05:13

  Labarai / Afirka

  'Yan Bindiga Sun Bude Wuta A Wani Massallaci Dake Kenya

  ‘Yan bindiga sun bude wuta a wani masallaci dake gabashin kasar Kenya, suka kashe a kalla mutane bakwai.

  Mazauna wata unguwa a lokacin da suke duba wani waje inda fashewar bom ta auku. Mazauna wata unguwa a lokacin da suke duba wani waje inda fashewar bom ta auku.
  x
  Mazauna wata unguwa a lokacin da suke duba wani waje inda fashewar bom ta auku.
  Mazauna wata unguwa a lokacin da suke duba wani waje inda fashewar bom ta auku.
  An kai harin ne yau alhamis a kauyen Maaleey, dake kusa da kan iyakar kasar Somaliya.
   
  Jami’ai a kasar sun ce an kashe mutane biyar a cikin masallacin yayinda aka kashe wadansu mata biyu lokacin da suka yi kokarin shiga masallacin da  gudu bayanda suka ji mutane suna ihu.
   
  Kawo yanzu babu kungiyar da ta dauki alhakin kai harin.
   
  Kenya tana fama da hare hare da suka hada da wadanda ake kaiwa da gurneti da ake dora alhakin kan mayakan al-Shabab na kasar Somaliya ko magoya bayansu.
   
  Kungiyar al-Shabab taci alwashin ramuwar gayya bayanda dakarun kasar Kenya suka shiga kudancin Somaliya a watan Oktoba shekara ta dubu biyu da goma sha daya da nufin yakar kungiyar kishin Islaman.

  Sauti

  • Shirin Dare
   Minti 30

   Shirin Dare

   A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

  • Shirin Rana
   Minti 30

   Shirin Rana

   Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

  • Shirin Hantsi
   Minti 30

   Shirin Hantsi

   Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

  • Shirin Safe
   Minti 30

   Shirin Safe

   Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

  • Shirin Dare
   Minti 30

   Shirin Dare

   A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

  Karin Bayani akan Shirya-shirye
  Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
  Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
   
  Karin Bayani akan Shirya-shirye