Talata, Satumba 01, 2015 Karfe 15:07

Labarai / Sauran Duniya

Manyan Kasashen Duniya Da Iran Na Shawarwari Dangane Da Nukiliya

Jami’ai manyan kasashen dunya shida da Iran suna shawarwari dangane da shirin nukiliuyar kasar da ke janyo gardama, a mataki na baya-bayan nan da nufin warware damuwa da ake da shi fiye da shekaru 10 cewa Iran tana kokarin kera makamin nukiliya.

Saeed Jalili, sakataren kungiyar tsaron Iran, tare da ministan harkokin wajen Kazakhstan, Yerlan Idrisov, Feb. 26, 2013Saeed Jalili, sakataren kungiyar tsaron Iran, tare da ministan harkokin wajen Kazakhstan, Yerlan Idrisov, Feb. 26, 2013
x
Saeed Jalili, sakataren kungiyar tsaron Iran, tare da ministan harkokin wajen Kazakhstan, Yerlan Idrisov, Feb. 26, 2013
Saeed Jalili, sakataren kungiyar tsaron Iran, tare da ministan harkokin wajen Kazakhstan, Yerlan Idrisov, Feb. 26, 2013
WASHINGTON, D.C - Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry yana kira ga Iran da ta rungumi difilomasiyya a kokarin warware burinta na Nukiliya.

Taron na yau Talata da ake yi a Almaty a Kazakhstan, ya hada kasashen nan biyar masu kujeru na din din din a kwamitin sulhu da Jamus, ba'a tsammani taron zai tabuka wani abu.

Ana jin manyan kasashen duniyan zasu yi wa Iran tayin sassauta takunkumin karya tattalin arziki da suka kakaba mata, idan ta yarda ta jingine inganta sinadaran Uranium.

Farisa dai ta dage cewa shirin Nukikliyarta na farar hula, amma kasashe masu a yawa a fadin duniya suna damuwar Iran tana da burin kera makamin Nukiliya ne.

Audio Shirin Safe:       1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Hantsi:    1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Rana:       1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Dare:       1530 - 1600 UTC

Audio Yau da Gobe:       1530 - 1600 UTC

Karin Bayani akan Sauti