Jumma’a, Afrilu 29, 2016 Karfe 20:45

  Labarai / Afirka

  'Yan Yawon Bude Idanu 19 Sun Mutu a Hadarin Jirgin Balon-Balo

  Wani jirgin ‘yan yawo bude ido mai siffar balom-balo yayi hadari kusa da birnin Luxor a Masar, kuma ya kashe ‘yan yawon bude ido su 19 da suke ciki.

  Samfurin jirgin balom-balo da ya fashe ran Fabrairu 26, 2013.Samfurin jirgin balom-balo da ya fashe ran Fabrairu 26, 2013.
  x
  Samfurin jirgin balom-balo da ya fashe ran Fabrairu 26, 2013.
  Samfurin jirgin balom-balo da ya fashe ran Fabrairu 26, 2013.
  WASHINGTON, D.C - Mutane biyu ciki harda matukin jirgin sun tsallake rijiya da baya, bayanda jirgin ya kama da wuta san nan yayi bindiga lokacin yana shawagi kamar mita 300 a sararin samaniya, a yammacin gabar tekun Nilu.

  Jami’ai suka ce mamatan sun hada da ‘yan kasar Faransa, Britaniya, da kuma wasu kasashe.

  Wuri da jirgin yayi hadari shine tsohon babban birnin Masar mai tarihi, wurin yana ganin tururuwar ‘yan yawon bude ido wadanda suke zuwa domin ganin dadaddun wuraren ibada, fadan sarakuna da kushewa, da suka hada da inda aka binne wani basarake ko fir’aunan nan da ake kira Tutankhamun.

  Tun a skerarar 1979 hukumar kula da al’adu da harkokin gargajiya ta Majalisar Dinkin Duniya UNESCO ta ayyana wurin a matsayin wuri mai dumbin tarihi a duniya.

  Sauti

  • Yau da Gobe
   Minti 30

   Yau da Gobe

   Yau da Gobe

  • Shirin Rana
   Minti 30

   Shirin Rana

   Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

  • Shirin Hantsi
   Minti 30

   Shirin Hantsi

   Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

  • Shirin Safe
   Minti 30

   Shirin Safe

   Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

  • Shirin Dare
   Minti 30

   Shirin Dare

   A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

  Karin Bayani akan Shirya-shirye
  Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
  Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
   
  Karin Bayani akan Shirya-shirye