Jumma’a, Satumba 04, 2015 Karfe 19:47

Labarai

Chuck Hagel Ya Zama Sakataren Tsaron Amurka

Karshen ta dai Chuck Hagel ya zama sakataren tsaron Amurka duk da kokarin da wasu 'yan Republican su ka yi na neman hana tabbatar da shi

Dan Republican kuma tsohon Sanata, Chuck Hagel wanda ya zama sabon sakataren tsaron AmurkaDan Republican kuma tsohon Sanata, Chuck Hagel wanda ya zama sabon sakataren tsaron Amurka
x
Dan Republican kuma tsohon Sanata, Chuck Hagel wanda ya zama sabon sakataren tsaron Amurka
Dan Republican kuma tsohon Sanata, Chuck Hagel wanda ya zama sabon sakataren tsaron Amurka
Halima Djimrao-Kane
Majalisar Dattawan Amurka ta kada kuri’ar tabbatar da nadin da shugaba Barack Obama ya yiwa Senata Hagel a matsayin sabon Sakataren Ma’aikatar tsaron Amurka.

A kuri’ar da ‘yan majalisar dattawan suka kada daren jiya Talata, masu goyon bayan sun sami rinjaye da kuri’u 58, wadanda basa goyon baya nada kuri’u 41.

Shugaba Barack Obama ya yaba da yadda ‘yan majalisar dattawan na Amurka suka kada kuri’ar amincewar da ya kira abinda yafi dacewa a lokacin da ake bukata.

Wata sanarwar da fadar shugaban Amurka ta White House ta bayar na bayyana Chuck Hagel a zaman tsohon soja mai kishin Amurka. Shi dai Chuck Hagel, tsohon dan majalisar dattawan Amurka ne mai wakiltar jam’iyyar Republican.
An rufe wannan dandalin
Sharhi/Ra'ayi
     
Babu sharhi ko daya har yanzu a kan wannan dandalin, rubuta guda domin zamowa na farko

Audio Shirin Safe:       1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Hantsi:    1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Rana:       1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Dare:       1530 - 1600 UTC

Audio Yau da Gobe:       1530 - 1600 UTC

Karin Bayani akan Sauti