WASHINGTON, D.C - A irin wannan zanga-zangar da suka gudanar a jiya a birnin Caracas, magoya bayan Mr. Capriles sun bi tituna suna ta buga kwannukan girki da kona shara a lokacinda suke neman lalle a sake kirga kuri’un da aka jefa a zaben.
‘Yansanda sun kalubalance su, har suka jefa musu barkonon tsohuwa don tarwatsa taron.
Ko bayan birnin na Caracas ance an gudanarda irin wannan zangazanga ta ‘yan adawa a wasu lardunan kasar.
An soma wannan rigingimmun ne jim kadan bayanda Hukumar zaben Veneuela ta tabattarda cewa Nicolas Maduro ne ya lashe wannan zaben da aka yi a ranar lahadin shekaranjiya.
Mr. Maduro, wanda marigayi tsohon shugaban venezulea Hugo Chavez da kansa ya zabo ya tsaida shi, ya lasher zaben da kuri’u kalilan ne: ya sami 50.7% yayinda Mr. Capriles ya tashi da 49.1%.