Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Britaniya Da Faransa da Jamus Sun Nemi A Yi Taron Gaggawa Kan 'Yan Ci Rani


Bakin haure a kasar Macedonia
Bakin haure a kasar Macedonia

A wannan watan ne kasar Macedonia ta ayyana kafa dokar ta baci a saboda yadda a kullum bakin haure har dubu 3 ke tsallakawa cikin kasar daga Girka a kan hanyarsu ta zuwa kasashen yammacin Turai.

Ministocin harkokin cikin gida na kasashen Britaniya, Faransa da Jamus sun yi kiran da a gudanar da taro na musamman na ministocin harkokin cikin gida da na shari’a na kasashen Tarayyar Turai cikin makonni biyu masu zuwa domin takalar matsalar ‘yan gudun hijira dake kara yin muni a nahiyar.

Ministocin sun fada cikin wata sanarwa a yau lahadi cewar su na son su samu kwararan matakai na warware wannan hali nab akin haure.

A baya cikin wannan watan ne kasar Macedonia ta ayyana kafa dokar ta baci a saboda yadda a kullum bakin haure har dubu 3 ke tsallakawa cikin kasar daga kasar Girka a kan hanyarsu ta zuwa kasashen yammacin Turai.

Yau lahadi a Macedonia, bakin haure su 500 suka shiga cikin wani jirgin kasa dake tafiya sau biyu a rana daga garin Gevgelija a kudancin kasar zuwa yankin bakin iyakar kudancin Macedonia a inda zasu iya tsallakawa zuwa cikin kasar Serbia.

Daga kasar Serbia, bakin hauren sukan shiga kasar Hungary a kan wannan hanya da ta bi ta tsaunukan Balkans zuwa yammacin Turai. Amma a jiya asabar, kasar Hungary ta bayyana cewa ta kammala kashin farko na katangar waya mai kaifin reza da take sanyawa a bakin iyakarta da kasar Serbia. Kamfanin dillancin labaran Faransa ya fada jiya asabar cewa ya zuwa yanzu dai, wannan Katanga mai tsawon kilomita 175 da aka kafa domin hana bakin hauren shiga cikin kasar, ba ta hana su tsallakawa cikin kasar ta Hungary ba.

Hungary ta bukaci da a dauki hoton zanen yatsun duk bakin haure kafin a shigar da su cikin sansanonin wucin gadi, abinda ya tayar da hankalin wasu.

Kasar Hungary ta zamo kadangaren bakin tulu a yunkurin ‘yan gudun hijirar na kaiwa ga kasashen turai ta yamma wadanda suka fi na gabashin nahiyar arziki a saboda tana rike su ta hana su shigewa, ko da wasu kasashen na yammacin turai sun yarda cewa zasu karbi wasu dubbai daga cikinsu.

XS
SM
MD
LG