Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Donald Trump Yanzu Yana Da Wakilai 950 Cikin 1237


Abokin hamayyarsa sanata Ted Cruz da gwamnan jihar Ohio John Kasich sun kudiri aniyyar takawa Trump burki.

Babban dantakarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar Republican Donald Trump, ya lashe zaben fidda gwani da aka yi a wasu jihohi dake arewa maso gabashin Amurka jiya Talata.

Trump ya sami nasara a saukake a jihohin Rhode Island, Delaware, Pennsylvania, Connecticut, da kuma Maryland.

Da ya ke magana ga magoya bayansa a daren jiya Talata, ya ayyana cewa "zaben fidda gwanin ya kare," kuma shine mutumin da zai sami tutar yiwa jam'iyyar Republican takara. Bayan zaben nan jiya Talata, Trump ya sami wakilai 950 cikin 1,237 da ake bukata domin zama dan takara, sai dai babu tabbas zai sami sauran wakilan nan lokacin da uwar jam'iyyar za ta yi babban taronta cikin watan Yuli.

Abokin hamayyarsa sanata Ted Cruz da gwamnan jihar Ohio John Kasich ba za su iya samun adadin wakilan da suke bukata ba amma duk da haka sun kudiri aniyyar takawa Trump burki.

A jam’iyyar Democrat kuma, tsohuwar sakatariyar harkokin wajen Amurka Hilary Clinton ta lashe hudu daga cikin jihohin nan biyar, watau Maryland, Pennsylvania, Delaware, da Connecticut. Abokin karawarta, Senata Bernie Sanders, ya sami nasarar lashe jihar Rhode Island.

Yanzu haka dai Hillary na da wakilai 2,141, ciki har da manyan wakilai da jam’iyya suka fidda wadanda suka dauki alkawarin za su mara mata baya. Saura wakilai 242 suka rage wa Clinton samun wakilan da jam’iyyar Democrat ke bukata don tsayar da dan takara.

Clinton ta gayawa gungun magoya bayanta a Philadelphia cewa, zata yi aiki domin hada kan jam'iyyar domin ta cimma nasara a babban zaben kasar cikin watan Nuwamba.

XS
SM
MD
LG