Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba Ranar Fara Jigilar Mahajjatan Kasar Jamahuriyar Nijer


Jirgin saman kasar Saudiyya
Jirgin saman kasar Saudiyya

A Kasar Jamahuriyar Nijer Maniyattan Aikin Hajjin Bana na cikin halin kila wa kala

Har yanzu dai ‘yan kasar Nijer maniyyata aikin Hajjin bana ba su san ranar da za su fara tashi ba, bayan da kamfanonin jigilar Mahajjata suka dage ranakun tashin da suka tsaida tun da farko.

Kafin wannan matsalar ta kunno kai dai da farin farko an ce da tun ranar takwas ga watan nan na Satumba Mahajjata ke fara tashi , a ci gaba da kwasar su zuwa kasar Saudiyya a ranakun tara da goma sha uku na watan Satumba.

Sai dai kuma duk kokarin da hukumomin kasar Nijer suka yi na neman yin rigakafin matsalolin dake tattare da shirya aikin Hajji, abun ya ci tura.

Kuma duk da wannan rashin tabbas yanzu haka maniyyata daga sassan kasar daban-daban sun cika Niamey babban birnin kasar makil, saboda galibi daga can aka saba kwasar su zuwa kasa mai tsarki.

Ga wakilin Sashen Hausa a birnin Niamey Abdoulaye Mamane Amadou da ci gaban rahoton.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:36 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG