Talata, Fabrairu 09, 2016 Karfe 16:46

  Labarai / Kiwon Lafiya

  Babban Bankin Duniya ya bukaci gwamnatocin kasashen Afrika su kara kaimi a yaki da HIV

  Bankin Duniya ya bukaci gwamnatocin Afrika su kara kaimi a shawo kan kamuwa da HIV

  Wani yana fama da cutar HIV
  Wani yana fama da cutar HIV

  Babban Bankin Duniya ya yi kira ga gwamnatocin kasashen nahiyar Afrika su kara kaimi wajen hana al’ummarsu ci gaba da kamuwa da cutar kanjamau.

  Babban Bankin Duniyan ya bayyana cewa, idan ba a dauki kwararan matakai ba, shawo kan cutar zai zama da wuya sakamakon karuwar masu kamuwa da cutar.

  Bankin ya kwatanta yaki da cutar shan inna da masu karbar kudin fansho, inda a kullum ake samun Karin wadanda suke shiga tsarin. Ya kuma shawarci gwamnatoci su kara kaimi wajen shawo kan yaduwar cutar.

  An sami Karin tallafin kudin da ake bayarwa a yaki da cutar kanjamau daga dala miliyan 260  a shekara ta 1996 zuwa biliyan 15 a shekara ta 2010. Sai dai babban magatakardar Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya yi kira ga masu bada tallafi su kara bada gudummuwa domin cimma burin tara kimanin dala biliyan 24 da aka kiyasta kashewa a shekara domin yaki da cutar HIV.

  Kasashen nahiyar Afrika sun ci gaba da kasancewa inda ake fama da cutar duk da yake nahiyar tana da kashi 12% ne kawai na adadin al’ummar duniya.

  Watakila Za A So…

  Yau da Gobe

  Yau da Gobe

  Yau da Gobe
  Shirin Rana

  Shirin Rana

  Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai da dumi-duminsu daga kowace kusurwa ta duniya, musamman ma dai muhimman abubuwan da suka faru, ko suke faruwa a kusa da ku a wannan rana.
  Shirin Hantsi

  Shirin Hantsi

  Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku da labarai da hirarraki, da sharhin jaridu kama daga Najeriya zuwa Nijar har Ghana, da kuma ra’ayoyinku.
  Shirin Safe

  Shirin Safe

  Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da rahotanni da dumi-duminsu, sannan mu na gabatar da wasu shirye-shirye kamar Noma da Lafiya Uwar Jiki.
  Shirin Dare

  Shirin Dare

  A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na yadda duniyar ta yini da rahotanni da dumi-duminsu, sannan mu kan bude muku layuka domin ku bugo ku bayyana mana ra’ayoyinku kan batutuwan da suka fi muhimmanci a wannan rana, ko kuma wadanda ke ci muku tuwo a kwarya.

  An rufe wannan dandalin
  Sharhi/Ra'ayi
       
  Babu sharhi ko daya har yanzu a kan wannan dandalin, rubuta guda domin zamowa na farko

  Sauti

  • Yau da Gobe
   Minti 30

   Yau da Gobe

   Yau da Gobe

  • Shirin Rana
   Minti 30

   Shirin Rana

   Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

  • Shirin Hantsi
   Minti 30

   Shirin Hantsi

   Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

  • Shirin Safe
   Minti 30

   Shirin Safe

   Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

  • Shirin Dare
   Minti 30

   Shirin Dare

   A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

  Karin Bayani akan Shirya-shirye
  Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
  Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
   
  Karin Bayani akan Shirya-shirye