Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bama-baman da Aka Boye Cikin Motoci Sun Kashe Mutane 30 a Iraqi


Wurin shan shyin 'yan shiya inda bam ya tashi
Wurin shan shyin 'yan shiya inda bam ya tashi

Bama-baman da suka tashi a wurin shan shayin 'yan shiya da unguwar kurdawa sun hallaka mutane da dama da jikata wasu

Hare haren bama bamai da aka boye cikin motoci sun kashe mutanen da yawansu ya kai talatin da bakwai a Iraq a jiya Alhamis. Ana kyautata zaton kila an auna kai hare haren ne akan 'Yan Shiya da Kurdawa.

Tashin bam na farko ya faru ne a shagon shan shayi a wata unguwar Kurdawa a birnin Kirkuk. Sa'anan kuma tashin bam na biyu ya faru ne a yankin birnin Sadr na birnin Bagadaza.

Kusan kullu yaumin ake kai hare haren ta'adanci a birnin Bagadaza da wasu biranen kasar Iraqi.

Kungiyar Islamic State ko IS a takaice tayi ikirarin cewa ita keda alhakin kai yawancin hare haren

A halin da ake ciki kuma, sabon jakadan Amirka a Iraqi, Stuart Jones yace sojojin Amirka suna da kariyar da ba za'a hukunta su a Iraqi ba.

Jakadan Jones ya shedawa kamfanin dilancin labarun Associated Press cewa ya samu wannan tabbaci daga Prime Ministan Iraq Haider Al-Abadi. Yace kariyar wani bangare ne, na jadawalin dabarar da aka shata tsakanin Amirka da Iraqi, daya tanadi sojojin Amirka zasu taimaka wajen baiwa sojojin Iraqi horo da kuma taimakon kayan aiki a kokarin da suke yi na murkushe yan yakin sa kan kungiyar IS.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG