Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Boko Haram ta Sace Mutane 20 a Kamaru


Rundunar sojojin Kamaru. (File Photo)
Rundunar sojojin Kamaru. (File Photo)

'Yan Boko Haram sun zafafa kai hare-hare a kasar Kamaru, inda su ka sace matafiya a mota su wajen 20 ciki har da mata a kalla 6.

‘Yan Boko Haram sun sace wasu mutanen kasar Kamaru akalla 20 da su ka je cin kasuwa a wani kauyen da ke daura da garin Goza na Nijeriya. Wakilin Muryar Amurka a Kamaru Danda Mamadu ya kuma ce ranar Litini sojojin Kamaru sun fafata da ‘yan Boko Haram a garin Kerawa, wanda ya yi sanadin jin raunuka ga sojojin Kamaru 10 a sa’ilinda su kuma sojojin su ka hallaka ‘yan ta’addan 11 baya ga motarsu guda da su ka kama.

Hasalima ‘yan ta’addan da su ka kara da sosojin Kamarun, ‘yan leken asiri ne da kuma duba hanyoyin da su ka fi saukin bi wajen kai harin daga wani gari mai suna Warawide, inda su ka ja daga. To amma sai su ka yi kicibis da sojojin Kamarun.

Danda Mamadu, ya ce a cikin mutane 20 da ‘yan Boko Haram su ka sace din har da ‘yan mata 6. Ya ce har yanzu dai ba a san komai game da makomar matan ba. Ya ce har yanzu sojojin Kamarun na cigaba da yaki da ‘yan Boko Haram din. Ya ce ana ta shirya gangamin nuna goyon baya da kuma karfafa gwiwa ga sojojin Kamarun a yakinsu da Boko Haram.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:35 0:00
Shiga Kai Tsaye

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG