Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bukatun 'yan Nijar daga 'yan siyasa


Jamhuriyar Nijar
Jamhuriyar Nijar

Muryar Amurka ta zagaya ta ji ra'ayoyin wasu 'yan Nijar akan abubuwan da suke son duk wanda ya zama shugaban kasa ya mayar da hankalinsa akai

A zagayawar jin ra'ayoyin jama'ar Nijar da Muryar Amurka ta yi, wakilinmu ya tattaro abubuwan da al'ummar kasar suka fada.

Malam Sule yace akwai abubuwa wadanda a matsayinsa na dan kasa suka dameshi. Duk shirye-shiryen da ya ji sun saba jinsu kuma basu taimakawa talaka ba. Babu wanda ya yi maganar samar da cimaka ma 'yan kasa ba tre da sai an shigo da abinci daga kasashen waje ba.

Alhaji Bubakar Musa yace duk 'yan siyasa su yiwa yaransu magana. Su daina musgunawa wasu ba ba sayi jam'iyyarsu. Kamata ya yi su yi nasu aikin su bar wasu su yi nasu. Taba kayan wasu dole ne ya jawo matsala. Su kuma sani cewa idan Allah ya basu jama'a babu mai iya kwacewa. Idan kuma bai basu ba babu karfin da zai basu.

Sule Umaru yace hamayya dole ta kawo hargitsi. Haka siyasa ta gada idan kuma an gama za'a koma a cigaba da rayuwa. Kawo yanzu dai ana gudanar da kemfen cikin kwanciyar hankali da fatan kuma akn haka za'a kammala.

Saidai wasu suna ganinhar yanzu babu dan takarar da ya ambato batun habaka harkokin yawon bude ido ko kuma illar dake tattare da canjin yanayi.

'Yan Nijar na bukatar gwamnatin da zata yiwa talakawa aiki ba kanta ba. Ta cirowa talaka hakinsa da 'yan siyasa suka danne.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:07 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG