Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

BURUNDI: Shugaba Nkurunziza Zai Sake Cin Zabe


Shugaban Burundi Nkururnziza
Shugaban Burundi Nkururnziza

Biyo bayan janyewa da 'yan adawa suka yi daga zabe shugaban kasa Shugaba Nkurunziza sai sake darewa karagar mulki karo na uku abun da kundun tasrin mulkinkasar ya haramta

A can Burundi ana sa ran shugaban kasar zai sake cin zaben shugaba karo na 3, yayinda ‘yan kasar ke kada kuri’a yau Talata a zaben da ‘yan adawa suka ki yi.

An dai cigaba da hidimar wannan zaben bayan watanni da aka kwashe ana zanga-zangar adawa da gwamnati da kuma yin kira ga kasashe akan shugaban ya koma gefe guda.

Masu suka sun ce bai cancanta shugaba Nkurunziza ya sake shugabancin kasar ba, amma kotun kundin tsarin mulkin kasar ta ce shugaban ya cancanta saboda ‘yan majalisa ne suka zabe shi, ba sauran jama’a ba a karon farko da yayi mulki.

Zanga-zangar da aka yi ta kai ga tashin hankali, ciki har da jin fashewar nakiyoyi da harbe-harbe a daren wata litinin a Bujunbura babban birnin kasar.

Sakatare Janar din Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya yi kira ga hukumomi da su tabbata an samar da tsaro da kuma kwaciyar hankali lokacin zaben, ya kuma yi kira ga duk jam’iyyun kasar da su koma kan teburin tattaunawa.

Masu bada shawara a Majalisar Dinkin Duniya na sa ido a zaben na yau Talata, wanda ya kunshi masu kada kuri’a miliyan 3.8. a kasar ta Burundi

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG