Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Canada zata janye jiragenta daga kai hari kan kungiyar ISIS


Firayim Ministan Canada Justin Trudeau
Firayim Ministan Canada Justin Trudeau

Kasar Canada zata fice daga kawancen da Amurka ke yiwa jagora wajen kai hari kan kungiyar ISIS a Syria da Iraqi

: Kasar Canada tace daga watan nan da muke ciki zata janye dukkan jiragen yakinta na sama daga cikin jiragen dake kai hare-hare akan sansanonin mayakan ISIS dake kasashen Syria da Iraq.

A jiya Litinin ne P-ministan Canada din, Justin Trudeau, yake bayyana cewa daga ran 22 ga watan nan Fabrairu ne Canada zata maido jiragenta shidda gida, wanda shine cikon alkawarin da ya dauka lokacinda yana kyamfen din neman zaman PM din a bara.

P-ministan yace hare-haren da ake kaiwa din suna da takaitaccen anfanin cimma burin da gamayyar kasashen da Amurka ke jagoranta ke nema, amma suna kuma da matukar lahani akan al’ummar yankunan da abin ya shafa.

XS
SM
MD
LG