Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

China Zata Wuce Jamus Sayar da Makamai


Firayim Ministan China Wen Jiabao
Firayim Ministan China Wen Jiabao

Wani rahot da ya fito ya nuna kasar China na gaf da wuce kasar Jamus a kan sayar da makamai.

Wani sabon bincike da aka fitar kan cinikin makamai a duniya ya nuna cewa kasar China ko Sin, wacce tattalin arzikinta shine na biyu a girma a duniya, tana neman ta zarce Jamus ta zama ta uku a duniya wajen sayar da makamai.

Wani rahoto daga cibiyar karfafa zaman lafiya dake birnin Stockholm na Sweden ya nuna kashi 70 na makaman da Sin ta sayar kasashen Pakistan da Bangladesh da Myanmar ne suka saye su. Haka nan kuma rahoton yace Beijing ta saidawa kasasehn Afirka 18 makamai. Alkaluman sun nuna cewa cinikin da Sin tayi ya karu da kamar kashi 143 tsakanin shekara ta 2005-2014.

Baki daya rahoton ya nuna cewa cinikin makamai a fadin duniya ya karu da kashi 16 cikin shekaru biyar da suka wuce.

Rahoton ya kuma nuna cewa Amurka ce take kan gaba wajen sayar da makamai inda ta sami karin kashi 23 cikin dari na cinikin makami cikin shekaru 10 da suka wuce. Makaman da Amurka ta sayar kashi 31 ne cikin dari na makamai da aka sayar tsakanin shekara ta 2010-zuwa 2014, sanan Rasha tana biye da ita da kashi 27.

Binciken ya nuna manyan kasashen da suka sayi makamai tsakanin 2010-2014 su ne India, Saudiyya, China, da hadaddiyar daular Larabawa, da kuma Pakistan.

XS
SM
MD
LG