Lahadi, Nuwamba 29, 2015 Karfe 15:05

Labarai / Sauran Duniya

Clinton Ta Fara Ziyarar Aiki Na Kwanaki 10 A Afirka

Talatan nan Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton ta tashi zuwa Senegal, kasa ta farko da zata yada zango a fara ziyarar aiki na kwanaki 10 a nahiyar Afirka.

Sakatariyar Harkokin wajen Amurka Hillary Clinton.
Sakatariyar Harkokin wajen Amurka Hillary Clinton.
Aliyu Imam

Talatan nan Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton ta tashi zuwa Senegal, kasa ta farko da zata yada zango a fara ziyarar aiki na kwanaki 10 a nahiyar Afirka, da zummar bunkasa matakan raya tattalin arziki da  demokuradiyya.

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta  ce sakatariya Clinton zata gana gobe laraba da sabon shugaban Senegal Macky Sal, kuma zata jinjina wa  Senegal a matsayin kasa wacce demokuradiyya ta sami zama da gindinta.

Mr. Sall sabon shugaban na Senegal, shine ya kada tsohon shugaban kasa Abdoulaye Wade a zaben da aka yi cikin watan Maris, bayan da  aka samu gardama kan ko shin ya cancanta tun farko ma Mr. Wade ya nemi wa’adi na uku.

Haka kuma ana sa  ran madam Clinton zata kai ziyara sabuwar kasa ta Sudan ta kudu,bayan ta balle daga Sudan a cikin shekarar da ta shige.

Ziyarar da zata kai Sudan din, tazo ne a lokacin da kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya yake muhawara kan irin matakai da  suka dace ya dauka na kawo karshen rikici kan rabon arzikin mai, batun  kan iyaka, da kuma batun zama dan kasa, matsaloli da suka ki ci suka ki cinyewa, tsakanin kasashen biyu.

An rufe wannan dandalin
Yadda Ake Son Gani
Sharhi/Ra'ayi
     
by: Adamu Dahiru Daga: Zaria
13.08.2012 14:36
Assalamu alaikum ma'aitan muryan Amurka.Ni dai sonake agano man hanya mafi sauki yadda za'a magance tsaro a nigeria.

Sauti

 • Shirin Hantsi
  Minti 30

  Shirin Hantsi

  Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

 • Shirin Safe
  Minti 30

  Shirin Safe

  Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

 • Shirin Dare
  Minti 30

  Shirin Dare

  A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

 • Shirin Rana
  Minti 30

  Shirin Rana

  Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

 • Shirin Hantsi
  Minti 30

  Shirin Hantsi

  Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

Karin Bayani akan Shirya-shirye
Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
 
Karin Bayani akan Shirya-shirye