Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cutar Sankarau ta Hallaka Yara da Dama A Kasar Nijar


Ciwon sankarau
Ciwon sankarau

Cutar Sankarau tayi sanadiyar mutane da dama a kasar Nijar.

Cutar ciwon sankarau naneman zama ruwan dare a kasar Nijar, a zuwa yanzu alkallunma na nuni da cewar kimanin mutane dubu shida da arba’in da tara ne, suka kamu da wanna cutar a wasu manya garuruwa da suka hada da Dogon Dutse, Gaya, Tawa, Doso duk a cikin kasar Nijar, wanda harma da babban birnin kasar na Niyame.

Kana kuma akalla mutane dari hudu da sha shidda ne suka rigamu gidan gaskiya, duk sana diyyar wannan cutar, hukumomi na iya kokarinsu su shawo kan wannan matsalar, tabakin Malam Mustapha Kadi, shugaban masu rajin kare hakkokin fararen hula a jamhuriyar Nijar in, yayi wadannan bayana, kuma yayi nuni da cewar suna kara kira ga al’uma da su tashi tsaye wajen ilmantar da mutane hanyoyi, da suka kamata su bi don magance wanna cutar a cikin al’uma.

Suna kara kiran jama’a da su yi kokari wajen samo magunguna da zasu bama yara don kaucema wanna annobar, duk dai da cewar sun lura wanna cutar ba kawai a kan yara ta tsaya ba, harma da manya suna bukatar taka tsan-tsan, don haka jama'a su isar da wannan sakon ga sauran danginsu a ko ina kamin wanna cutar ta kaiga wuce hannu.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG