Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Da Zaton Harin Jirgin Sama Ya Raunata Shugaban Daular Islama


Mayakan ISIL
Mayakan ISIL

Ana zaton harin jirgin sama da Amurka ke yi ya raunata shugaban Daular Islama Abu Bakr al-Baghadi

Wasu manyan jami'an gwamnatin Iraki sun ce jagoran kungiyar Daular Islama, Abu Bakr al-Baghdadi, ya ji rauni a wani harin jirgin sama, to amma hedikwatar tsaron Amurka ta Pentagon tace ba ta da masaniya kan hakan.

An ce Ministan Tsaron Iraki Khalid al-Ubaydi, ya wallafa wani bayani a shafinsa na dandalin sada zumunci na FaceBook, inda ya tabbatar cewa al-Baghdadi ya ji rauni sanadiyyar wani harin jirgin saman Amurka na ranar Jumma'a a birnin Mosul na arewacin Iraki.

Ma'aikatar Cikin Gidan Iraki ma ta tabbatar da wannan labarin ga kafar Associated Press. Wasu kafafen labarai da dama kuma sun ce harin jirgin saman ya hallaka daya daga cikin hadiman al-Baghdadi

Tun da farko a jiya Lahadi, wani babban jami'in sojan Burtaniya ya yi gargadin cewa ko da ma labarin gaskiya ne, kungiyar ta Daular Islama za ta sake farfado da shugabancinta. Hafsan Hafsoshin sojin Burtaniya Nick Houghton ya fadi a wata hira da kafar labarai ta BBC cewa kodama an kashe al-Baghdadi, ba zai yi saurin ayyana cewa wani babban koma baya ne ga mayakan ba.

Ya ce, "Ba zan iya hakikance cewa an kashe al-Baghdadi ba. Ko Amurkawan kansu ba su da wannan tabbacin. Mai yiwuwa ya dan ranaku kafin a iya tantancewa. Abin da ba zan so yi ba shi ne in gaggauta nuna cewa mutuwar wani jigonsu za ta haifar da wani komabaya cikin kungiyar. Za su sake kafa shugabanci. Wannan ko zai faru ne saboda ban-sha'awar da wannan shu'umar akida ke da shi, sai ko idan za mu iya katse dabarunsu a siyasance, idan ba haka ba lallai ISIS na iya cigaba da sake murmurewa da kuma sake kafa shugabancinta."

A wata hira a shirin "Face the Nation" na kafar labarai ta CBS da ke nan Amurka, Shugaban Amurka Barack Obama ya ce hare-haren jirgin saman da ake kaiwa na tasiri sosai wajen rage karfin mayakan da kuma rage saurinsu.

Ya ce tura karin sojojin Amurka 1,500 zuwa Iraki da zai yi,don su bada horo ma sojojin Iraki, wani babi ne aka shiga na yaki da 'yan Daular ta Islama. Mr. Obama ya ce ribanya sojojin Amurka zai taimaki Iraki ta kaddamar da wasu hare-haren, to amma ya nanata matsayinsa na cewa sojojin Amurka ba za su shiga yakin kasa ba.

XS
SM
MD
LG