Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dakarun Iraqi Da Na Shi'a Sun Tunkari Ramadi


A jiya Juma’a, kungiyar ta IS ta dauki alhakin kai wasu hare-hare a yankunan kasashen larabawa, wadanda suka hari masallatan ‘yan Shi’a.

Wata sabuwar kungiya mai ikrarin alaka da kungiyar ta IS ta ce ita ke da alhakin wani hari da aka kai a gabashin Saudi Aarabia dake karkashin gwamnatin Qatif, harin da ya halaka mutane 21 ya kuma raunatu akalla mutum tamanin.

Wani hari na biyu kuma a kusa da wani masallaci a Sana’a babban birnin kasar Yemen ya raunatu mutane 13.

Wadannan hare-hare sun kara adadin mutanen dake jikkata a wajen ksashen Syria da Iraqi da yawanci mayakan na IS ke kai hari.

Yanzu haka, mataimakin shugaban kasar Iraqi, Ayad Allawi, ya fara dasa alamar tambaya kan hare-haren sama da Amurka ke jagoranta akan ‘yan kungiyar ta IS.

A lokacin da ya ke wani jawabi a wani taron duba tattalin arzikin duniya a Jordan, Mr Allawi, ya ce akwai bukatar a sauya salon yaki da ‘yan kungiyar, ganin irin bunkasar da su ke samu duk da hare-haren da ake kai musu.

Wadannan kalamai na mataimakin shugaban kasar ta Iraqi, na zuwa ne mako guda bayan da mayakan na IS suka karbe ikon Ramadi.

A tsakanin Alhamis da jiya Juma’a dakarun hadin gwiwa sun kai hare-haren sama guda biyar yayin da wasu samamen suka karkata akan matattarar mayakan dake Mosul da kuma birnin Ramadi dake karkashin ikonsu.

XS
SM
MD
LG