Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dukkan Yaran Dake Jihar Edo Zasu Yi Rigakafin Cutar Polio Nan Da Karshen Shekarar Nan


Gwamna Adams Oshiomhole yace tilas ne dukkan yaran dake cikin jihar su samu rigakafin Polio da na sauran cututtuka kafin karshen wannan shekara.

Gwamna Adams Oshomhole na Jihar Edo yace tilas a bayar da rigakafin cutar shan inna ta Polio da sauran cututtukan da ake iya rigakafinsu ga du yaran dake cikin jihar nan da karshen wannan shekara.

Gwamna Oshiomhole yana magana ne talata a karshen sabon zagayen aikin rigakafin kwanaki hudu na kasa baki daya a Benin.

Yace wannan aiki yana da matukar muhimmanci kum atilas ne kowa ya bayar da hadin kai domin cimma gurin gudanar da shi.

Ya roki al’ummar jihar da su hada kai domin tabbatar da cewa an kai wannan sako kowane lungu na jihar.

Ya yabawa ma’aikatar kiwon lafiya ta Jihar da sauran hukumomi da kungiyoyi saboda kwazon da suka nuna wajen yin rigakafin da ya sa rabon da a samu bullar cutar Polio a Jihar ta Edo tun shekarar 2009, shekaru biyar da suka shige.

Kwamishinar kiwon lafiya ta Jihar Edo, Dr Aihanuwa Eregie, ta ce an samu nasarar bayar da rigakafin na Polio ga yara fiye da dubu 618 daga cikin yara kusan dubu 797 da aka yi niyyar bas u, watau kimanin kasha 78 daga cikin 100 na yaran jihar a zagayen na wannan mako.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG