Talata, Maris 31, 2015 Karfe 00:00

Sauran Duniya

Firai Ministan Japan ya gargadi China ta kare rayuka da kaddarorin al'umarsa

Masu zanga zanga a kofar ofishin jakadancin JapanMasu zanga zanga a kofar ofishin jakadancin Japan
x
Masu zanga zanga a kofar ofishin jakadancin Japan
Masu zanga zanga a kofar ofishin jakadancin Japan
Firai Ministan kasar Japan Yoshihiko Noda ya yi kira ga China ta tabbatar da kare lafiyar al’ummar kasar Japan da cibiyoyin kasuwancinsu a China, yayinda aka shiga kwana na biyu ana zanga zangar nuna kin jinin Japan a China.

An fara zanga zangar ne sakamakon matakin da Japan ta dauka na mallakar tsibirai dake tekun gabashin China da ake takaddama a kai.

Dubban mutanen kasar China suka yi zanga zanga a kofar ofishin jakadancin Japan dake birnin Beijing jiya asabar, inda suka rika jifa da duwatsu  suka kuma kona tutocin kasar Japan. Zanga zangar ta bazu zuwa biranen kasar China da dama.

Wannan tarzomar ita ce ta baya bayan nan a jerin zanga zanga da aka fara gudanarwa tun ranar Talata bayan da Japan tace ta sayi tsibiran daga hannun wanda ya mallake su. China tace wannan cinikin biri a sama ne, yayinda take ikirarin mallakar yankin.

Rikicin ya yi zafi ranar jumma’a lokacin da China ta tura jiragen sa ido shida, suka yiwa tsibiran da ba wanda ke zaune a wurin da ake kira Diayu dake kasar China da kuma Senkaku dake kasar Japan  kawanya.

Audio Shirin Safe :         0500 - 0530 UTC

Audio Shirin Hantsi :      0700 - 0730 UTC

Audio Shirin Rana :        1500 - 1530 UTC

Audio Shirin Dare :         2030 - 2100 UTC

Audio Yau da Gobe:       1530 - 1600 UTC

Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12026190548 ko kuma +12026190551.
Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
 
Karin Bayani akan Sauti