Juma'a, Yuli 03, 2015 Karfe 13:18

Afirka

Firai Ministan Kasar Kenya Zai Tsaya Takarar Shugaban Kasa

Firai Ministan kasar Kenya Raila OdingaFirai Ministan kasar Kenya Raila Odinga
x
Firai Ministan kasar Kenya Raila Odinga
Firai Ministan kasar Kenya Raila Odinga
Firai Ministan kasar Kenya Raila Odinga ya bayyana cewa zai tsaya takarar shugaban kasa a watan Maris mai zuwa.

Mr. Odinga zai wakilci kungiyar hadin guiwa mai da’awar garambawul da ake kira Coalition for Reform and Democracy ko CORD a takaice. Mr Odinga ya tsaya takara da shugaba mai ci yanzu Mwai Kibaki a shekara ta dubu biyu da bakwai, zaben da ya haddasa tashin hankalin da ya yi sanadin mutuwar dubban mutane.

Mataimakin shugaban kasa Kalonza Musyoka memban CORD ya bayyana sha’awar tsayawa takarar shugaban kasa, sai dai ya sanar jiya asabar cewa, ba zai yi hamayya da Mr. Odinga ba.

Wani wanda kuma zai tsaya takarar shugaban kasar shine, mataimakin PM Uhuru Kenyatta wanda kotun bin kadin laifuka ta kasa da kasa ke tuhuma da laifin kuntatawa bil’adama a tashin hankalin da aka yi tsakanin shekara ta dubu biyu da bakwai zuwa dubu biyu da takwas da ya biyo bayan zaben da ake zargin an tafka magudi.

Ana ganin zaben da za a gudanar a shekara ta dubu biyu da goma sha uku a matsayin zakaran gwajin dafi a siyasar kasar Kenya.

Audio Shirin Safe:       1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Hantsi:    1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Rana:       1530 - 1600 UTC

Audio Shirin Dare:       1530 - 1600 UTC

Audio Yau da Gobe:       1530 - 1600 UTC

Karin Bayani akan Sauti