Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gidauniyar Lawrence Ellison Ta Shiga Cikin Yaki Da Polio


Gidauniyar zata bayar da gudumawar Dala Miliyan 100 a gwagwarmayar karshe ta kawar da Polio daga duniya

Ganin irin nasarar da aka samu wajen rage yawan masu kamuwa da cutar Polio a Najeriya da Afghanistan, biyu daga cikin kasashe uku da suka rage da cutar Polio a duniya yanzu haka, Gidauniyar Lawrence Ellison ta bayarda sanarwar gudumawar dala miliyan 100 cikin shekaru biyar domin tallafawa yunkurin kawar da wannan cuta baki dayanta.

Gidauniyar ta riga ta mika kimanin dala miliyan 20 na wannan gudumawa a shekarar 2013. Wannan gudumawa zata tallafawa Shierin kawar da Polio daga duniya wanda ya tsara jadawalin kawar da cutar daga duniya cikin shekaru 6 a kan kudi Dala biliyan 5 da rabi.

Shigar Gidauniyar Lawrence Ellison cikin wannan yunurin ya kawo adadin manyan masu bayarda agaji su 10 wadanda suka yi alkwarin bayar da dala miliyan 535, a bayan gudumawar kudi dala miliyan dubu 1 da 800 da Bill Gates, daya daga cikin shugabannin Gidauniyar Bill da Melinda Gates yake bayarwa daga 2013 zuwa 2018 domin kawar da wannan cuta.

A wurin Taron Kolin Rigakafi na Duniya da aka yi a watan Afrilun bara a kasar Abu Dhabi, gwamnatoci da attajirai fiye da 35, ciki har da Gidauniyar Gates sun yi alkwarin bayar da dala mili8yan dubu 4 domin tallafawa wannan kokarin, ganin cewa an fara ganin hasken iya kawo karshen wannan cuta da kawar da ita har abada daga doron duniya.

Bill Gates yace, “Shirin Kawar Da Cutar Polio daga Duniya ya kawo mu dab da bakin gacci. Mun san cewa wannan mataki na karshe shi ne zai zamo mafi wahala, kuma bai kamata a ce rashin kudi da kayan aiki sun kawo mana cikas wajen cimma wannan gagarumar nasara ta kawar da shan inna daga duniya baki day aba. Wannan babbar gudumawa ta Larry Ellison zata taimaka wajen tabbatar da cewa an kare dukkan yaran duniya daga shan inna da sauran cututtukan da ake iya karewa ta hanyar rigakafi.”

A shekarar 2013, a bayan da aka yi shekara guda ana ganin raguwar yaduwar Polio kamar yadda ba a taba gani a can bay aba, wannan shirin ya fuskanci kalubale a saboda an kasa yin rigakafi ga yara a wasu yankunan da ake fama da rashin tsaro a arewacin Najeriya da arewa maso yammacin Pakistan. Haka kuma an samu bullar cutar a kasashen sda a can baya babu su inda kuma ake fama da fitina, a yankin kuryar gabashin Afirka da kuma kasar Sham. Amma duk da wannan kalubale, an ci gaba da samun nasara a yunkurin kawar da cutar.

A Najeriya, an samu raguwar kasha 57 cikin 100 na masu kamuwa da Polio a 2013, yayin da a kasar Afghanistan aka samu raguwar kasha 65 cikin 100.

Kasar Indiya, ta cimma tazara sosai domin ta cika shekara uku ba tare da an samu bullar cutar Polio ko guda day aba.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG