Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gubar Dalma Tana Da Illa Ga Kananan Yara


Kwararrun lafiya a Najeriya su na binciken cutar gubar dalma
Kwararrun lafiya a Najeriya su na binciken cutar gubar dalma

Najeriya na daya daga cikin kasashen da kananan yara suke fuskantar matsalar gubar dalma, abinda aka danganta da talauci da kuma rashin sanin matakan kare yara daga kamuwa da cutukan da gubar dalma ke sawa.

Najeriya na daya daga cikin kasashen da kananan yara suke fuskantar matsalar gubar dalma, abinda aka danganta da talauci da kuma rashin sanin matakan kare yara daga kamuwa da cutukan da gubar dalma ke sawa.

Daya daga cikin jihohin da ake fama da gubar dalma ita ce jihar Zamfara inda jami’an kiwon lafiya na kasa da kasa suka bayyana cewa kananan yara 100 sun kamu da cutar da ake dangantawa da gubar dalma.

Gubar dalma tana sa kananan yara kamuwa da ciwon koda ko wadansu muhimman kayan ciki. Yawan gubar dalma yana iya sa kananan yara suma ko kuma mutuwa. Idan gubar bata yi yawa a jikin yaro ba kuma tana iya sawa ya zama dakiki ko ya ya kurmance ko ya shafi yanayin rayuwarshi ko kuma wadansu matsaloli dabam dabam.

Idan gubar dalma ta shiga jinin yaro, yakan zama koma baya gareshi duk tsawon rayuwarshi, sai dai sau da dama ba a banbanta illar gubar da wadansu cucutuka ko koma baya da wanda ya kamu da cutar ya samu a rayuwarshi.

Bisa ga bayanin likitoci, hanyar raba kananan yara daga kamuwa daga cutar ita ce daukar matakin ganin kananan yara basu taba wani abu ko sutura da ke da gubar ba da ake dauka daga kurar dake dauke da gubar, ko sutura, ko turbaya ko ruwan da ya gurbace ko duk wani abu dake dauke da gubar.

Kasashe da cuka ci gaba kamar Amurka sun dade da daukar matakan shawo kan matsalar tare da kafa dokar da ta haramta amfani da dalma a fenti ko fetir da dai makamantan haka.
XS
SM
MD
LG