Litinin, Mayu 02, 2016 Karfe 04:38

  Labarai / Najeriya

  Gwamna Adam Oshimole Ya Sami Gagarumar Nasara A Edo.

  Bayan yakin neman zabe cike da hayaniya, da suka hada da zargin magudin zabe, jama'a a jihar Edo yanzu suna rawa da sowa akan tituna.

  Kungiyar 'yan kwadago ta Najeriya suke maci. Kungiyar da Gwamna Oshimole yayi wa jagoranci a baya
  Kungiyar 'yan kwadago ta Najeriya suke maci. Kungiyar da Gwamna Oshimole yayi wa jagoranci a baya
  Aliyu Imam

  Bayan yakin neman zabe cike da hayaniya, da suka hada da zargin magudin zabe, jama'a a jihar Edo yanzu suna rawa da  sowa akan tituna.

  Hukumar zabe tace Gwamna mai ci Adam Oshimole, na jam'iyyar 'yan hamayya ya sami babban rinjaye  a zaben gwamna da aka yi ranar Asabar.

  Masu fashin bake suka ce nasarar da 'yan hamayya suka yi a yankin da ya zame tamkar tungar  jam'iyyar dake mulkin kasar PDP, ba alama ce mai kyau ga shugaba Goodluck Jonathan ba.

  Jiragen yaki masu saukar ungulu suna ta shawagai a wajajen rumfunan zabe jiya Asabar, da tsammanin za  a sami rikici. Dubban sojoji kuma suna sintiri kan tituna da kuma a rumfunan zabe. Amma ba a fuskanci wani tarzoma mai tsanani da aka sami labari ta auku ba.

  A safiyar lahadin nan, bayan da aka bayyana sakamakon zaben gwamnan, mutane suka fantsama akan tituna suna rawa ana kuma ruwan sama.

  Hukumar zabe ta Najeriya tace Gwamna Oshimole ya sami kashi 73.7 na yawan kuri'u da aka kada, ita kuma jam'iyyar PDP mai mulkin kasar ta sami kashi 22.3. Sauran kashi 4 da ya rage sauran jam'iyyu suka raba tsakaninsu.

  Wani manomin doya da rogo, Emmanuel Igbinedon, yace wan nan zaben shine zakaran gwajin dafi a jihar ta Edo.

  "Wan nan  zabe shine wanda aka gudnar cikin lumana fiyeda ko wanne da aka taba yi. "Kuma wan nan zabe ya koya mana darasin cewa ba a sayen kuri'a".

  Kamin zaben, duka jam'iyun biyu suna ta zargin juna na kitsa magudi da tarzoma, wadanda  suka hada da hayan masu kisan gilla. Har zuwa lokacinda ake kidaya kuri'u ma, gwamnan jihar ya zargi hukumar zabe cewa da gangan ta makara kai kayan zabe da kuma cire sunayen masu zabe a kundin  sunayen masu kada kuri'a. Kuma tayi haka ne tareda hadin bakin jam'iyyar PDP mai mulkin kasar.

  Wata kungiyar tallafi mai zaman kanta mai cibiya a Abuja tace tayi aiki da dubban masu aikin sa ido a jihar, wadanda suka  ce an sami nasarar a zaben da  aka gudanar da aka nuna  adalci, duk da 'yan matsaloli da aka fuskanta.

  Da yake magana, babban darektan kungiyar Clement Nwankwo, yace sakamakon zaben wata babbar koma baya ce ga jam'iyyar dake mulkin Najeriya a tarayya, domin jihar Edo tana cikin yankin "kudu maso kudu", inda  daga yankin ne shugaba Jonatahan yake da  mafi yawan goyon baya.

  "Nasarar da dan takarar ACN ya samu babba ce, kuma ta kasance manuniya kan zubewar farin jinin da  shugaba Jonathan yake da shi, inji Nwanko.

  'Yan hamayya suka ce nasarar da aka samu ana jiya jingina ta kan wani hadin kai tsakanin 'yan hamayya, kuma sunyi alkawarin  zasu hada karfi wajen ganin sun kada Jam'iyyar PDP a zaben shugaban kasa, a 2015.

  Watakila Za A So…

  Matar tsohon shugaban Ghana zata tsaya takarar shugaban kasar

  Jam'iyyar adawar kasar Ghana National Democratic Party ko NDP ta tsayar da matar tsohon shugaban kasar Nana Konadu Agyeman-Rawlings a matayin 'yar takararta a zaben shugaban kasar da za'a yi. Karin Bayani

  Sauti Rikici ya raba jam'iyyar PDP gida biyu a jihar Adamawa

  Wata sabuwar badakala ta kunno kai a jam'iyyar PDP game da zaben matakin anguwanni a jihar Adamawa lamarin da ya sa ta rabe gida biyu. Karin Bayani

  Sauti PDP ta tura mukamin dan takarar shugaban kasa arewa a zaben 2019

  Jam'iyyar PDP ta amince zata tura mukamin dan takarar shugaban kasa zuwa arewa a zaben 2019 idan Allah ya kaimu har da ma na shugaban jam'iyyar Karin Bayani

  Sauti Akwai jituwa tsakanin gwamnatin Borno da ma'aikata

  Yayinda ake birkin ranar ma'aikata jiya mataimakin gwamnan Borno Alhaji Usman Mamman Durkuwa yace akwai hadin kai da jituwa tsakanin ma'aikatan jihar da gwamnati Karin Bayani

  Tsaftar Ruwa Babbar Fa’ida Ce - Arc Abdullahi

  An lura cewa wata hanyar kare mutane daga cututtuka masu yawa ita ce tabbatar da tsafta, da lafiya da kuma ingancin ruwanda su ke sha. Karin Bayani

  Yau Ce Ranar Ma’aikata Ta Duniya

  Kamar kowace shekara, wannan shekarar ma ma'aikata a fadin duniya sun bayyana korafe-korafensu a wannan rana ta ma'aikata ta yau. Karin Bayani

  An rufe wannan dandalin
  Sharhi/Ra'ayi
       
  Babu sharhi ko daya har yanzu a kan wannan dandalin, rubuta guda domin zamowa na farko

  Sauti

  • Shirin Rana
   Minti 30

   Shirin Rana

   Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

  • Shirin Hantsi
   Minti 30

   Shirin Hantsi

   Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

  • Shirin Safe
   Minti 30

   Shirin Safe

   Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

  • Shirin Dare
   Minti 30

   Shirin Dare

   A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

  • Shirin Rana
   Minti 30

   Shirin Rana

   Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

  Karin Bayani akan Shirya-shirye
  Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
  Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
   
  Karin Bayani akan Shirya-shirye