Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Kasar Mali Na Binciken Kasancewar Cutar Ebola

Ma'aikatar kiwon lafiya suna binciken cutar Ebola
Ma'aikatar kiwon lafiya suna binciken cutar Ebola

Jami'an gwamnatin kasar Mali na binciken rashin lafiyar wasu mutane uku da ake zaton cutar Ebola ce, a jiya Jumm'a ministan lafiyar kasar Mali ya bada sanarwar mutanen uku, a daidai lokacin da kasashen yankin ke fama da bullar mummunar cutar mai kisa.

Ma'aikatan lafiya sun dauki samfurin wasu abubuwa daga jikin marasa lafiyar su ka tura su zuwa wani dakin binciken birnin Atlanta, a nan Amurka, domin a yi gwaje-gwaje a kan su. A halin da ake ciki kuma, yanzu haka an kebe mutanen uku an killace su, a inda ake yi mu su jinya.

Hukumar lafiya ta Duniya, WHO, ta fada a jiya Alhamis cewa hukumomin kasashen yammacin Afirka sun bada rahoton da ya tabbatar da cewa mutane fiye da dari da talatin ne su ka kamu ko kuma ake zaton sun kamu da cutar Ebola, akasarin su a kasar Guinea.

Hukumar ta WHO ta ce cutar ta yi sanadin mutuwar mutane tamanin da uku a Guinea, biyar kuma a kasar Laberiya.

Wata kwayar cuta mai saurin yaduwa ce ke haddasa ciwon Ebola, da ke bazuwa ta hanyar taba abubuwan da ke fita daga jikin dan Adam kamar su yawu, majina, bawali, bayan gida, jini da makamantan su.

Kwararrun masana harakokin kiwon lafiya su na gargadin jama'ar da ke zaune a yankunan da aka samu bullar cutar, da su guji yin ma'amala kai tsaye da wadanda suka kamu da cutar ko kuma suka rasu sanadiyar ta.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG