Jumma’a, Nuwamba 27, 2015 Karfe 09:12

Labarai / Kiwon Lafiya

Gwamnatin Najeriya ta Bada Kyautar Maganin Cutar Kwalara ga Jihar Nasarawa

Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta bada kyautar magunguna ga gwamnatin jihar Nassarawa domin ta kare yaduwar cutar kwalara da zazzabin lassa a jihar.

Ruwan sha mai tsabta
Ruwan sha mai tsabta
Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta bada kyautar magunguna ga gwamnatin jihar Nassarawa domin ta kare yaduwar cutar kwalara da zazzabin lassa a jihar.

Yayinda yake mika magungunan ga ma’aikatar lafiya ta lafia a madadin gwamnatin tarayya, babban mai binciken yaduwar cututtuka na Ma’aikatar lafiya ta tarayya Akin Oyemakinde yace kyautar magungunan wani yunkuri ne na gwamnatin tarayya domin kawas da yaduwar cutar kwalara da zazzabin lassa a jihar Nassarawa.

Akin Oyemakinde, wanda ya jagoranci kungiya daga ma’aikatar lafiya ta gwamnatin tarayya zuwa jihar, ya baiyyana cewa sun je ne domin kawo daukin gaggawa, domin hana yaduwar cutar zuwa wasu sassa na jihar da kuma jihohin dake makwabtaka da jihar Nasarawa wanda ya zama abun damuwa ga gwamnatin tarayya.

Ya kuma ce wannan kungiyar taje da manufar ganin irin daukin da jihar take bayaswa ga bullowar kwalara da kuma irin shirin da take da shin a hana yaduwar cutar, su kuma kara sa ido akan wannan matsalar. Ya kara da cewa, wani aikin wannan kungiya shine taimakon jihar don inganta shirinta domin sake barkewar cutar kwalara.

Yayinda yake kira ga gwamnatin jihar ta fadakar da mutane musamman na karamar hukumomi kan hadarin kwalara, ya gargadi gwamnatin jihar ta karfafa aiyyukan taimako, tanajin ruwa mai kyau ga mutane da kuma bayanai kan tsabta, lafiya da yadda za’a shirya abinci mai tsabta.

Shima da yake Magana a lokacin, Fatai Oyediran, wanda shine mataimakin direkta a ma’aikatar lafiya ta kasa ya lura cewa ma’aikatar ta koyar da kimanin ma’aikatan lafiya guda dari da suka hada da masu sa ido kan yanayin lafiya, masu allurar rigakafi musamman kan zazzabin lassa. Ya kuma kara da cewa horaswar ta bada kari ne kan koyawa ma’aikatan lafiya hanyoyin da zasu iya gane barkewar wadannan cututtuka da kuma irin daukin da zasu iya bayaswa.

Yayinda yake yi wa gwamantin tarayya godiya, a nashi bayanin, kwamishinan lafiya na jihar Nassarawa, Emmanuel Akabe, wanda ya karbi magungunan a madadin gwamnatin jihar, ya baiyyana kyautar a matsayin wani babban taimako da zai kauda cutar kwalara da zazzabin lassa a jihar.

Kwamishinan lafiya ya bayyana cewa gwamnatin jihar Nassarawa ta hada hannu da wata kungiyar kasar Amurka domin yin wani wurin yin bincike akan zazzabin lassa da kuma masassarar tsuntsaye wadda ya zuwa yanzu an rigaya an sa hannu a takardar fahimta.

Wani ruhoto da gwamnatin jihar ta bayar ya nuna ya zuwa yanzu, an sami kimanin masu cutar kwalara 306 an kuma sami mace mace 16 a jihar. Ya kuma ci gaba da cewa an sami labarin barkewar kwalara na farko a jihar a Satumba 2013 a kananan hukumomin Akwanga, Wamba, Lafia, Awe, Obi da karu.

“Magungunan da gwamnatin tarayya ta bayar sun hada da: ringers lactate, dextrose, calcium hypochloride, erythomycin, doxcycline capsule ORS da ribavarin," inji shi.

Watakila Za A So…

Shirin Hantsi

Shirin Hantsi

Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku da labarai da hirarraki, da sharhin jaridu kama daga Najeriya zuwa Nijar har Ghana, da kuma ra’ayoyinku.
Shirin Safe

Shirin Safe

Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da rahotanni da dumi-duminsu, sannan mu na gabatar da wasu shirye-shirye kamar Noma da Lafiya Uwar Jiki.
Shirin Dare

Shirin Dare

A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na yadda duniyar ta yini da rahotanni da dumi-duminsu, sannan mu kan bude muku layuka domin ku bugo ku bayyana mana ra’ayoyinku kan batutuwan da suka fi muhimmanci a wannan rana, ko kuma wadanda ke ci muku tuwo a kwarya.
Shirin Rana

Shirin Rana

Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai da dumi-duminsu daga kowace kusurwa ta duniya, musamman ma dai muhimman abubuwan da suka faru, ko suke faruwa a kusa da ku a wannan rana.

An rufe wannan dandalin
Sharhi/Ra'ayi
     
Babu sharhi ko daya har yanzu a kan wannan dandalin, rubuta guda domin zamowa na farko

Sauti

 • Shirin Hantsi
  Minti 30

  Shirin Hantsi

  Mu kan komo da karfe 8 na safe agogon Najeriya da Nijar domin sake gabatar muku...

 • Shirin Safe
  Minti 30

  Shirin Safe

  Kullum da karfe 6 na safe agogon Najeriya da Nijar muna gabatar da labarai da...

 • Shirin Dare
  Minti 30

  Shirin Dare

  A shirin namu na karfe 9 da rabi agogon Najeriya da Nijar, zaku ji labarai na...

 • Yau da Gobe
  Minti 30

  Yau da Gobe

  Yau da Gobe

 • Shirin Rana
  Minti 30

  Shirin Rana

  Da karfe 4 na yamma agogon Najeriya da Nijar zaku iya jin rahotanni da labarai...

Karin Bayani akan Shirya-shirye
Lambobin bayyana ra'ayoyi a shirinmu na dare: +12022052655
Lambar kira don bayyana ra'ayi ko yaushe ake so: +12022059942.
 
Karin Bayani akan Shirya-shirye